Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar gundumar mazaɓar Kebbi ta Arewa ya bai wa haɗaɗɗiyar ƙungiyar manoma ta jihar Kebbi tirela biyu na takin zamani.
Da ya ke hannanta takin ga shugabannin ƙungiyar a madadin Sanatan, Alhaji Bara’u Abubakar Abdullahi ya bayyana cewa Sanata a ko da yaushe shirye ya ke da ya kawo duk wani abu na cigaba wanda al’umma za ta amfana da shi ba tare da nuna bambancin siyasa ba.
Ya ƙara da cewa tallafawa al’umma ya zama wajibi ga duk wani ɗan ƙasa nagari da ke riƙe da wani matsayi musamman wanda al’umma suka zaɓa don shugabanci ko kuma wakilci.
Ya bayyana ƙungiyar manoma a matsayin uwar ƙungiyoyi saboda noma shi ne ginshiqin zama lafiya.
Shugaban ƙungiyar manoma ta jihar Kebbi Alhaji Usman Ɗangwandu Suru ya yaba wa Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi bisa ga irin wannan taimakon da ya ke yi savanin inda aka fito saboda a tarihin ‘yan siyasa ba a tava samun wani ɗan siyasa da ke aiwatar da irin wannan ba.
Ya bayyana cewa zaɓen irin Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi ba shakka babu da na sani a cikin sa saboda haka ‘yan siyasa ya kamata su yi koyi da shi musamman wajen yin abinda ya kamata a lokacin da ya kamata.
Ya kuma yi alqawarin za a zauna tare da duk wanda ke da ruwa da tsaki a cikin wannan ƙungiyar don tabbatar da an raba takin yadda ya kamata.