Sanata Yahaya ya ja kunnen ‘yan siyasa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Sanata  mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa kuma Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi ya ja kunnen ‘yan siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani abu da zai tayar da husuma a lokacin bukin cikar Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera shekaru ashirin da biyar kan karagar mulki da kuma naɗin sarautu da za a gudanar a fadar Sarkin Kabin ranar Juma’a 5 ga wannan watan.

Wannan yana ƙunshe ne a wata takarda da aka raba wa ‘yan jarida mai ɗauke da sa hannun Muhammed Jamil Yusuf Gulma, mataimaki na musamman kan harkar yada labarai na sanatan.

Takardar ta bayyana cewa bayan bukin cikar Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera shekaru ashirin da biyar kan karagar mulki, akwai kuma naɗin sarautun Maigirma Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan a matsayin Ganuwar Kabi da kuma Sanata Kalu Orji Kalu a matsayin Kibiyar Kabi.

Akwai baƙi na musamman da aka gayyato daga wurare daban-daban a faɗin ƙasar nan saboda haka kamar yadda aka san mutanen jihar Kebbi da ɗa’a da karimci da son zaman lafiya, ana fatar su nuna wannan halin nasu da aka san su da shi.

Bayan taya sarki murnar cikar shekaru ashirin da biyar kan karagar mulki ya kuma yi fatar sabon Ganuwar Kabi da Kibiyar Kabi da su kasance jakadun wannan masarauta a duk inda suka samu kawunansu.