Sanatoci sun karɓi shaidar lashe zaɓensu

Daga BASHIR ISAH

A ranar Talata Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga sanatocin da suka yi nasara a zaɓen da ya gabta.

Shugaban INEC na ƙasa, Mahmood Yakubu, shi ne ya jagoranci miƙa shaidar ga sanatocin wanda ya gudana a Babban Zauren Taro na Ƙasa da Ƙasa da ke Abuja.

A jawabin da ya yi ran Asabar da ta gabata, Yakubu ya ce 423 ne suka lashe kujerun majalisun tarayya, yayin da za a sake zaɓe a wasu mazaɓu 46.

Waɗanda suka yi nasarar sun haɗa da sanatoci 98 daga cikin 109 da ake da su, sai kuma ‘yan Majalisar Wakilai 325 daga cikin 360 da ake da su.

Game da ‘yan majalisun da za su kafa majalisa ta 10, Shugaban na INEC ya ce, APC ta lashe kujerar sanata 57, PDP – 29; LP – 6; SDP – 2; NNPP – 2; YPP – 1; dai kuma APGA – 1.

A ɓangaren Majalisar Wakilai kuwa, APC na da kujera 162; PDP – 102; LP – 34; NNPP – 18; APGA – 4; ADC – 2; SDP – 2; YPP – 1.