Sanatocin Arewa sun gargaɗi ECOWAS kan amfani da ƙarfin soji a Nijar

Daga BASHIR ISAH

Sanatocin Arewa sun gargaɗi Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan aiki da ƙarfin soji wajen maido da dimokuraɗiyya a Jamhuriyar Nijar.

Sanatocin ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdul Ahmad Ningi (Bauchi), sun ce amfani da tsarin diflomasiyya ne mafita wajen dawo da gwamnatin dimokraɗiyya a ƙasar ta Nijar.

Cikin sanarwar da sanatocin suka fitar ta bakin kakakinsu, Suleiman A. Kawu Sumaila, sun yi gargaɗin amfani da ƙarfin soji zai haifar da asarar rayuka a ƙasar Nijar da maƙwabtanta.

Sanarwar ta ce, “Ba mu yarda da amfani da ƙarfin soji ba har sai an gama bin hanyoyin da muka ambata a sama, saboda amfani da ƙarfin soji zai haifar da asarar rayukar waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.

“Hakan ka iya shafar kimanin jihohin Arewa bakwai da ke maƙwabtaka da Jamhuriyar Nijar da suka haɗa da Sakkwato Kebbi, Katsina, Zamfara, Jigawa, Yobe da kuma Borno.