Sani Sha’aban ne zaɓin al’ummar Kaduna a 2023 – Ƙungiyar SSSG

Daga ABDU LABARAN a Zariya

An bayyana Hon. Sani Mahmood Sha’aban ,(Ɗan Buran Zazzau, a matsayin mutum ɗaya tilo da zai iya fitar da Jihar Kaduna daga cikin mawuyacin halin da ta samu kanta ciki.

Wannan jawabi ya fito ne daga bakin ɗaya daga cikin jiga-jigan ‘yan Ƙungiyar Sani Sha’aban Support Group (SSSG), Malam Ibrahim Auwal.

Ya ce “abun baƙin ciki ne da takaici yadda al’ummar Jihar Kaduna suka samu kansu a halin ko-in-kula da rashin aikin yi da durƙushewar kasuwanci da taɓarɓarewar harkar kiwon lafiya da tsaro.

Ibrahim Auwal ya ƙara da cewa, yanzu babu wata mafita da ta wuce ɗauko Hon. Sani Mahmood Sha’aban domin ya zama Gwamnan Jihar Kaduna, don ya kawo canjin aa ake buƙata mai ma’ana.

A ƙarshe, matashin ya ce ba za su ƙara bari a yi musu sakiyar da ba ruwa ba, kuma ƙungiyar SSSG ta shirya jajircewa wajen tabbatar da Hon. Sani Mahmood Sha’aban ya zama Gwamnan Jihar Kaduna a zaɓe mai zuwa don ya kawo wa jihar nagartaccen canjin da ta ke buƙata ta fannoni da dama.

Sannan sai ya yi kira ga al’umar jihar da su mara wa gogan nasu baya inda a ranar 11 ga Afrilu, 2022 zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kaduna a babban zaɓe na ƙasa mai zuwa a 2023 a hukumance.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *