Sannu a hankali wasannin ƙanƙara na samun karɓuwa a ƙasar Sin

Daga CRI HAUSA

Tun bayan ƙasar Sin ta fara shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022, an gudanar da wasannin ƙanƙara iri daban-daban na jama’a, a wurare daban-daban na ƙasar. Kana an gina wuraren wasannin ƙanƙara masu kyau, waɗanda suka sa ƙaimi ga ƙarin mutane zaɓar shiga wasannin ƙanƙara. Yanzu, Sinawa na iya wasannin motsa jiki a duk shekara, ko lokacin zafi ko kuma lokacin sanyi.

Wasannin motsa wata hanya ce ta kyautata zaman rayuwar jama’a. Bisa ƙididdigar da aka yi, yawan mutanen da su kan motsa jiki a birnin Beijing ya kai kashi 50.18 na adadin mutanen birnin baki ɗaya.

Ban da wannan kuma, gwmnatocin biranen Beijing da Zhangjiakou, sun gabatar da wasu ƙa’idoji da shirye-shirye don samarwa mutane masu buƙatun musamman hidimomi don taimaka musu a zaman rayuwa daga fannonin hanyoyin motoci, da zirga-zirgar yau da kullum, da wuraren samar da hidima, da musayar ra’ayoyi, da dai sauransu.

Ya zuwa watan Disamban shekarar 2021, ɗakunan kula da mutane masu buƙatun musamman na birnin Beijing guda 666 sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da hidimomi ga mutane masu buƙatun musamman, inda suka hidimtawa mutane masu buƙatun musamman miliyan 3 da dubu 914.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *