Sanwo-Olu ya nuna rashin jin daɗinsa kan soke amfani da yarukan gida a makarantu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi Allah-wadai da ƙin amincewa da koyarwa cikin yarukan gida a makarantu, wanda a cewarsa, shi ne farkon matsala a tsakanin al’umma.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a taron da Cibiyar JRandle ta shirya a wani gidan tarihin Fasaha da Al’adu ta Yarbawa a Onikan.

Gidan tarihin, wanda ya ƙunshi kayayyakin tarihi da dama na al’adun Yarabawa, wani muhimmin ɓangare ne, wanda aka ƙaddamar a bara.

Sanwo-Olu ya jaddada cewa muhimmancin Cibiyar ta JRandle na da dabarun alaƙar tarihin Nijeriya.

A cewarsa “Da juyin mulkin da ‘yan mulkin mallaka suka yi, wasu daga cikin mu sun ɗan samu wargajewa, Legas ta kasance wurin tarihi mai ƙarfi har lokacin da Nijeriya ta kafu, sai da muka koma tsohuwar yankin yammacin Legas, wanda daga nan ne aka samu Surulere, Ikeja, da sauransu.

Gwamnan ya kuma naɗa ƙudus Onikeku a matsayin Daraktan Cibiyar.

Da yake jawabi a wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar ƙirƙire-ƙirƙire a Cibiyar JRandle Onikan Legas, gwamnan ya ce jihar ta kasance cibiyar yawon buɗe ido kuma tana da damar yin kaɗe-kaɗe, fina-finai, fasaha da al’adu a Afirka.