Saraki ya halarci ɗaurin suren ɗiyar Sheikh Bala Lau

Daga NASIRU S. GWANGWAZO

A yau Juma’a ne tsohon Shugaban majalisar dattawan Nijeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Kwara, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya halarci ɗaurin auren diyar shugaban kungiyar Izala ta Nijeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Auren wanda aka ɗaura a babban masallacin Juma’a na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi dake unguwar Malali a Jihar Kaduna ya samu halartar manyan mutane da malamai daga sassan Nijeriya.

Wazirin na Ilorin ya shaidi auren wanda aka kulla tsakanin amarya Rufaida Bala Lau da angonta Tijjani Abdullahi Gabba.

A wani saƙon taya murna da ya ɗora a shafinsa na Facebook, Dakta Saraki ya yi wa ma’auratan fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya albarkaci aurensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *