Sarakunan Machina, Nguru da Bade sun sha alwashin mara wa sojoji baya kan yaƙi da matsalar tsaro

Daga BASHIR ISAH

Sarkin Machina, Alh Dr. Bashir Albishir Bukar (OON) da na Nguru, Alh Mustapha Ibn Mai Kyari da kuma Sarkin Bade, Alh Mai Abubakar Umar Suleiman, baki ɗayansu a Jihar Yobe, sun sha alwashin mara wa sojoji baya don ci gaba da yaƙi da matsalolin tsaro musmaman a shiyyar Arewa maso Gabas.

Sarakunan sun bayyana hakan ne sa’ilin da dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) mai yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas ta kai musu ziyara a ranar Talata.

Rundunar ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Mayirenso Lander David Saraso, ta ziyarci sarakunan ne domin ci gaba da neman haɗin kansu game da sha’anin yaƙi da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.

A jawabin sarakunan, kowannensu ya bai wa rundunar tabbacin ci gaba da samun haɗin kan da ya dace daga gare su don murƙushe matsalar tsaro a yankunansu da ma sauran sassan ƙasa.

Kazalika, sun yaba wa rundunar dangane da yadda ta yi aikinta wanda hakan ya taimaka wajen gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na majalisun tarayya cikin kwanciyar hankali a yankunansu.

A nasa ɓangaren, Manjo Janar Saraso, ya ce sun yi ziyarar ne domin ƙarfafa zumuntar da ke tsakanin rundunar da masarautun.

Jami’in ya ƙara da cewa, irin wannan ziyarar al’ada ce ta rundunar inda sukan ziyarci iyayen ƙasa don neman haɗin kansu kan abin da ya shafi ayyukansu.

Waɗannan bayanai na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labaran da kakakin rundunar, Kyaftin Kennedy Anyanwu ya fitar a ranar Alhamis.