Sarki Charles (III), Musulunci da Sufanci: Sharhi a kan Bayanan Khalifa Muhammadu Sunusi (II)

Dafa FATUHU MUSTAFA

In mai karatu yana zaton zai ga na yi bayani akan alaƙar gidan sarautar Ingila da Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam) ne, to sai in ce ya daɓo a ƙasa. Domin ba abinda ya kawo ni ba kenan. Ƙila idan na samu lokaci, nan gaba zan yi wannan bayanin. Amma a yanzu abinda yafi ɗaukar hankali

na shi ne, bayanin da Sarkin Kano, Halifa Muhammadu Sunusi ya yi ne a hirar sa da gidan rediyon RFI akan alaƙar diplomasiyya da ke tsakanin sabon Sarkin Ingila wato Sarki Charles III da addinin Islama, musamman alaqarsa da sufaye.

Masana sun tabbatar da, Sarki Charles tun yana Yarima, mutum ne mai shaawar addinin Islama. Anyi ittifakin ba wani a gidan sarautar Ingila da ya kai shi sanin addinin Musulunci.

Sha’awar da addinin ce ma ta sanya har ake kallon sa a matsayin ‘Islamophilia’, wato waɗanda ba musulmai ba, amma suna da son da kuma sha’awar addinin. Cikin abubuwan da ya sanya ake masa wannan kallo, sun hada da:

Ya koma makaranta domin koyon larabci, saboda ya ƙara wa daɓensa na ilmin addini makuba. Kuma a duk sarakunan Ingila, shi ne na farko da aka tabbatar yana jin harshen larabci.

Sarki Charles bai tsaya anan ba, ya kafa wata kwaleji dake nazartar fasahar musulunci, Royal Institute of Islamic Art, wacce ke bai wa ɗalibai dama su nazarci fasahar musulmai a matakin digiri na biyu (Masters Degree).

Haka kuma, shi ne uban tafiyar kwalejin nazarin addinin musulunci ta katafariyar Jamiar nan ta Oxford. Hakan ya sanya ya ɗauki nauyin karatun matasa musulmai da dama, a kan dabarun shugabanci da zamantakewa.

Sarki Charles (III), an tabbatar da cewa, yana da sha’awar ilmin sufanci, har ma ya taɓa yin mubayi’a ga Sheikh Nazim Al- Haƙƙani, wani bijmin jagora na ɗariƙar Naqshabandi ɗan ƙasar Turkiya, da yayi shuhura tsakanin 1974 zuwa mutuwar sa a 2014.

Wannan dalili ne ya sanya, wasu masana ke zargin cewa, a zahiri dai jagoran ɗariƙar Anglican ce ta kirisranci, amma a baɗini ba a iya rabewa da baccin makaho.

Hakazalika, akwai kuma kyakkyawar alaƙa a tsakanin gidansu da wasu gidajen manyan malaman addinin musulunci a ƙasar Hausa. Wanda hakan ta ƙara danƙon zumunci mai ɗorewa har ‘ya’ya da jikoki. Musamman a Kano da Zariya.

Wani babban abin sha’awa game da alaƙarsa ta addini shi ne, yayin da ake yi wa Sarakunan Ingila laƙabin ‘Defender of the faith’, shi Sarki Charles ya nemi da a cire kalmar “the” a rinka sanya masa Defender of faith. Wannan ya nuna ƙarara, a yanzu Sarki Charles ya zama uba ga dukkan addinai ba kawai addinin Kirista ba. Hakan kuma ba zai rasa nasaba da irin kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da addinin islama ba.

To amma fa duk wannan abubuwan da na zayyano, akwai wani hanzari ba gudu ba, ba a yabon ɗan kuturu sai ya girma da yatsun sa.

Allah ya taimaki Sarki, ya kuma ja da ran sarki amin!

Fatuhu Mustafa marubuci ne, kuma mai sharhin al’amuran yau da gobe. Ya rubuto ne daga Abuja.