Sarkin Borin Kabi ya zama Garkuwan masu maganin gargajiya na ƙasa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu bayar da maganin gargajiya ta ƙasa ta zaɓi Yusuf Abubakar a matsayin Garkuwan masu maganin gargajiya na ƙasa.

Tawagar ta masu maganin gargajiya ta ƙasa da ta reshen jihar Kebbi ta iso fadar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera a ƙarƙashin jagoranacin Malam Bala Hassan inda suka tabbatar wa Masarautar Sarkin Kabin Argungu da cewa wannan zaɓen Allah ne, sun zaɓe shi ne tun daga mataki na ƙasa ba tare da wata jayayya ba saboda la’akari da irin rawar da ya ke takawa a wannan ɓangaren.

Da ya ke jawabi Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera ya yabawa wannan kungiyar da ta yi wannan tunanin, ba shakka Malam Yusuf Abubakar ya cancanci kowane irin matsayi a wannan ɓangaren saboda mu ke tare da shi mu ne muka san irin ayukan da ya ke yi, tabbas haziki ne da ba a taba saka shi a wani lamarin da ya shafi harkarsa ba da ba samu nasara ba.

Ya ja hankalin masu bayar da maganin gargajiyar da su saka tsoron Allah a cikin wannan sana’ar ta su, kowa ya san abinda ya ke iyawa saboda haka duk lokacin da wani mutum ya zo da wata matsala musamman a vangaren rashin lafiya to a gaya masa gaskiyar lamarin kada a saka yaudara a ciki.

Ba shakka wannan sana’ar ta maganin gargajiya daɗaɗɗiyar sana’a ce da ke da tarihi a ƙasashen Afrika da har yanzu ba a sake ba saboda yanzu haka a waɗansu ƙasashe za ka ga an buɗe shaguna ba abinda ke ciki sai magungunan gargajiya da suka haɗa da saiwa, ganye, vawo da dai sauransu, wannan duk sanadiyyar jajircewar masu bayar da maganin gargajiya ne, kuma sai da yawa a kan yi amfani da su a samu waraka.

Sabon garkuwan masu bayar da maganin gargajiya Malam Yusuf Abubakar ya yaba wa Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera bisa ga irin karimcin da ya ke nuna musu na sauraronsu a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso tare da ba su shawarwari.

Ya kuma gode wa shugabannin ƙungiyar bisa ga tunanin zaƙulo shi a ba shi wannan matsayin.

Ya kuma yi alƙawarin cigaba da bayar da tasa gudummawa kamar yadda ya saba tare da neman haɗin kan ‘ya’yan wannan ƙungiyar don cigaban wannan sana’ar ta su.