Sarkin Kano, Aminu Bayero ya yi fatan a yi zaɓuɓɓuka lafiya

Daga RABIU SANUSI a Kano

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya buƙaci al’ummar Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya da su kasance masu ƙaunar zaman lafiya yayin zaɓuɓɓukan da za a gudanar da ma bayansu.

Sarkin ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da jawabi na musamman ga manema labarai a fadarsa.

Ya ce sai da zaman lafiya ake iya aiwatar da komai, don haka ya buƙaci matasa su guji furta munanan kalamai da ta’ammali da makamai da shaye-shaye don kaucewa daga fadawa mummunan hali.

Basaraken ya kuma jaddada buƙatar hakimai da dagatai da masu unguwanni su ci gaba da wayar da kan al’ummarsu muhimmacin zaman lumana.

Kazalika, ya yi kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da sa ido tare da hukunta duk wanda ya aikata ba daidai ba.

A ƙarshe, Sarki Aminu ya yi addu’ar samun zaɓin shugabanni nagari a dukkan matakan zaɓuɓɓukan da za a gudanar a faɗin ƙasar nan.