Sarkin Kano ya ziyarci Sarkin Katsina kan batun ajiye muƙamin Wazirin Katsina, Farfesa Lugga

Daga BASHIR ISAH

A jiya Lahadi Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da takwaransa na Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman suka yi wata ganawar sirri inda suka shafe sama da sa’a guda suna tattaunawa a fadar Sarkin Katsina.

Duk da dai babu wani cikakken bayani game da ganawar sarakunan ya zuwa haɗa wannan rahoton, sai dai ana kyautata zaton cewa ganawar na da nasaba da batun ajiye muƙamin da Wazirin Katsina, Farfesa Sani Abubakar Lugga ya yi kwanan nan.

Yayin da yake jawabi a wajen wani taro da ya halarta a Illorin, Jihar Kwara a ranar 14 ga Fabrairu, Farfesa Lugga ya yi tsokaci kan irin ƙalubalen da ƙasar nan ke fama da shi, musamman ma jiharsa, Katsina.

Lamarin da ya sanya masarautar Katsina ta aika masa da takarda tana mai neman bayani daga gare shi kan abin da ya sa ya yi wancan tsokaci musamman kan abin da ya shafi wasu ɓangarori guda uku.

Ɓangarori ukun da masarautar ke nufi sun haɗa da bayanin da Wazirin ya yi kan cewa makarantu da sauran cibiyoyi na wasu yankunan ƙananan hukumomi takwas a Katsina na cikin haɗari. Da kuma cewa da ya yi aƙalla mutum guda ake kashewa kulli yaumi a Katsina a sama da shekara gudan da ta gabata, sannan cewa dakattan ƙananan hukumomi takwas ɗin da lamarin ya shafa duk sun ƙaura sun koma babban birnin jihar.

Waɗannan kalamai da wazirin ya yi su ne aka ce ba su yi wa masarautar daɗi ba wanda hakan ya sa ta tura masa da takardar neman bayani.

Duk da dai Wazirin ya amsa takardar da masaraurar ta aika masa, amma ya haɗa amsar tasa tare da wasiƙar ajiye muƙaminsa sannan ya miƙa ma masarautar.

A cikin wasiƙarsa zuwa ga masarautar, Farfesa Lugga ya nuna cewa bayanin da ya yi a wajen taron, ya yi ne a matsayinsa na ɗan ƙasa mamma ba wai a madadin masarautar ba.

Wata majiya da ta sami jin ta bakin Sarkin Kano dangane da ziyarar tasa ta ce, wasu masu faɗa a ji daga Arewa ne suka wakilta Sarkin Kano don yin ziyarar da zummar shiga batun ajiye muƙamin da Wazirin ya yi.

Sai dai babu wani cikakken bayani kan ko an cimma wata yarjejeniya a tattaunawar da sarakunan biyu suka yi, amma dai majiyar jaridar Daily Trust ta ce shiga lamarin da Sarkin Kano ya yi wata alama ce mai ƙarfi da ke nuni da za a cimma daidaito.