Sarkin Musulmi ba na Sokoto ba ne kawai ba, Shettima ya gargaɗi gwamnatin jihar Sokoto

Daga Umar Garba a Katsina

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Kashim Shettima ya gargaɗi gwamnatin jihar Sokoto game da wasu rahotanni dake bayyana cewar gwamnatin jihar ta tura wata doka zuwa majalisar dokokin jihar wadda za ta rage wa Sarkin Musulmi ƙarfin iKon da yake da shi ko kuma ta kore shi daga kan kujerar ta sa.

” Sarkin Musulmi ba na Sokoto ba ne kawai ba, kujera ce wadda wajibi ne dukkanmu mu kare ta, mu ɗaukaka ta don amfanin ƙasa.” Inji shi.Shettima ya bayyana haka ne a wajen taron haɗin gwiwa wanda gwamnonin jihohin arewa maso yamma haɗin gwiwa da hukumar jinƙai ta majalisar ɗinkin duniya (UNDP) ta shirya a jihar Katsina, don inganta yanayin tsaro a jihohin waɗanda ke fama da matsalar ‘yan bindiga.

Sai dai wannan kalamai na mataimakin shugaban ƙasar ya ɗauki hankalin gwamnatin jihar Sokoto dama sauran ‘yan Najeriya musamman mazauna yankin arewa duba da rikicin sarautar jihar Kano da har yanzu ake ta muhawara a kansa.

A martanin da gwamnatin jihar Sokoto ta mayar wa Shettima, cikin wata takardar da Blueprint Manhaja ta gani, gwamnatin jihar ta ce kamata ya yi Shettima ya tuntuɓi gwamnan jihar game da lamarin don tantance gaskiyar labarin da ake yadawa na sauke Sarkin Musulmi, ba wai ya fito a bainar jama’a yana magana ba.Cikin takardar wadda mai magana da yawun gwamna Ahmad Aliyu, Abubakar Bawa ya sa wa hannu ta ce,”Mu na tsammanin Mataimakin Shugaban ƙasa zai tuntuɓi gwamna kafin furtar maganar a bainar jama’a.

“A matsayin sa na mai faɗa a ji kuma uba ga kowa ya kamata ya tantance sahihancin labari kafin ya yanke hukunce.” Inji sanarwar.A cewar shi masu amfani da shafukan sada zumunta ne ke ƙirƙirar waɗannan labarai don ɓata sunan gwamnatin jihar.

“Gaskiyar magana ita ce ba bu wani shirin tsige Sarkin Musulmi kuma ba a aike da wata doka ba game da haka.”Sarkin Musulmi ya na samun dukkan wani iko da ya kamata, ba mu taɓa hana shi wani haƙƙi ko ‘yancin ba.”Saboda haka babu buƙatar a faɗa mana cewar mu kare shi ko mu martaba kujerarsa, wannan haƙƙin mu ne. Inji kakakin gwamnan.

Leave a Reply