Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato
Tsohon Ministan sadarwa da fasaha, Farfesa Isa Ali Pantami OON, ya samu sabuwar sarauta a Daular Usmaniyya, wadda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar CFR, mni, ya bashi a lokacin rufe babban taron makon Ɗanfodiyo karo na 11, wanda aka gudanar a Sakkwato.
Taron wanda ya gudana a ranar Asabar da ta gabata, ya haɗo kan malamai da manazarta da sarakuna daga ciki da wajen Nijeriya.
Da yake sanar da wannan naɗi na sarautar majidaɗin Daular Usmaniyya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya ce an bada ita ne saboda yabawa da yadda shahararren malamin addinin Musuluncin yake bada gudunmawa ga cigaban al’amuran addini da ƙasa baki ɗaya da kuma tallafawa talakawa wajen neman ilimi. Sannan ya ƙara nuni da yadda babban malamin yake nuna kulawa da ƙauna ga abubuwan da suka shafi Daular Usmaniyya.
Sabon Majidaɗin Daular Usmaniyya, wanda ya bayyana godiyarsa da wannan babban tukwici da aka ba shi, ya kuma gabatar da lacca mai taken, “Haɗin kai a matsayin hanyar magance matsalar tsaro da talauci.