Sarkin Sasa ne ya naɗa ni Ƙauran jihohin Kudu – Aminu Kuceri

Daga DAUDA USMAN a Legas 

Ƙauran jihohin kudu da yammacin Nijeriya, Alhaji Aminu Bature Kuceri, ya bayyana cewar Sarkin Sasa a Ibadan, Alhaji Malam Haruna mai Yasin Katsina ne ya naɗa shi a matsayin sarautar Ƙauran jihohin kudu da yammacin Nijeriya a Legas.

Alhaji Aminu Kuceri ya faɗi hakan ne a gidansa na kallon wasan damben gargajiya da ke unguwar  Alabar Rago a lokacin da ƙungiyar ta su ta gudanar da wani ɗan ƙwarya-kwaryar taro kuma yake bayyana kaɗan daga cikin tarihin rayuwarsa.

Kuceri ya cigaba da cewar baya ga wannan sarautar ma da Sarkin Sasa Ibadan ya ba shi ta Ƙauran kudu da yammacin Nijeriya, akwai waɗansu sarautun guda biyu wanda ɗaya daga ciki baban sa maigarin Kuceri ya naɗa shi a matsayin Jarman Kuceri ta biyu kuma abokin baban nasa mai garin Kuncin Kalgo ya naɗa shi a matsayin  Baraden Ƙuncin Kalgo, da fatan Allah Ubangiji  ya jiƙan su da rahama.

Da yake tsokaci akan sana’ar su ta gidajen kallon wasan damben gargajiya a halin yanzu, ya ce damben gargajiya ya samu ci gaba domin kuwa suna nan suna ƙoƙarin ganin cewar an sanya wasan damben a cikin tsarin wasannin ƙasashen Turawa da ake alfahari da su har ma ana kallonsu a waɗansu kafofin yaɗa labarai. Ya ce akan haka ne ma ƙungiyar tasu take gudanar da tarurruka a kai-a kai tare da `yan wasan damben gargajiya domin wayar masu da kai tare da nuna masu illar shaye-shayen ƙwayoyi a wajen ɗan wasa.

 Ya ƙara da cewa kuma da zaran sun gama tabbatar da wannan al’amari bada daɗewa ba  za su haramta wa duk wani ɗan wasan damben gargajiya shan ƙwayoyi hatta sigari da makamantansu, kamar yadda sauran ƙungiyin wasanni na duniya suka sanya wa ‘yan wasan su doka a game da shaye-shaye.

Kuceri ya cigaba jawo hankulan ‘yan wasan na damben gargajiya da su riƙe sana’arsu hannu bibiyu kafin su kai lokacin da za su riqa samun milyoyin kuɗi kamar yadda waɗansu ƙasashen duniya suke samu. A ƙarshe ya yi fatan Allah ya cigaba da zaunar da Nijeriya lafiya da al’ummar cikinta bakiɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *