Saudiyya ta ayyana gobe Laraba a matsayin hutun aiki sakamakon doke ƙasar Argentina

Daga IBRAHIM HAMISU

Sarki ƙasar Saudiyya Salman bin Abdul Aziz, ya ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu a faɗin ƙasar wani mataki na murnar samun nasara da tawagar ‘yan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar suka samu a kan ƙasar Argentina.

An dai tashi wasan ne Saudiyya ta samu nasara a kan Argentina da ci 2-1 a wasan farko da suka buga a filin wasa na Lusail.

Ƙasar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanar wa da ta fitar a ranarTalata.

Sanarwar ta ce, Sarkin ya bayar da hutun ne domin ‘yan ƙasar tun daga ma’aikatan gwamnati da ma’aikatu masu zaman kansu har ma da ɗaukacin ɗalibai su gudanar da murnar nasarar da tawagar ƴan wasan ƙasar ta samu kan ‘yan wasan ƙasar Argentina a gasar ƙwallaon ƙafa ta cin kofin duniya da ake gudanarwa yanzu haka a ƙasar Qatar.