Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Hukumomin Ƙasar Saudiyya sun cafke ‘yan Nijeriya guda 20 bisa laifukan ta’ammali da baza hotunan wani mai neman shiga takarar shugabancin Nijeriya a harabobin Harami dake garin Makka ta ƙasa mai tsarki.
A halin da ake ciki dai, waɗannan ‘yan Nijeriya suna damƙe a hannun mahukuntan ƙasar ta Saudiyya ƙarƙashin kulawa da askarawan ƙasar kafin gurfanar da su a gaban kuliya manta-sabo, inda za a yi masu hukunce-hukunce daidai da laifukan su.
Wata majiya mai tushe ta shaidar da cewar, waɗannan ‘yan Nijeriya da suka shiga cikin halayyar aikata sharo ba shanu, za su ɗanɗana kuɗar su matuƙar an gurfanar da su a gaban kuliya.
Hukumomin na ƙasar Saudiyya sun ce faufau ba za su lamunci ire-iren wannan halayya ta ‘yan Nijeriya ba da suka saɓa wa tsari ko dokokin ƙasar su, kuma sun ce sam ba su san da irin wannan halayya ba.
Binciken da wakilin mu ya gudanar na ƙoƙarin samun sunan ɗan neman takarar shugabancin Nijeriya da ake yaƙin neman zaɓe da hotunan a garin Makka ya cimma tura, amma bayanai sun yi nuni da cewar, akwai wani ɗan neman shiga takara daga shiyyar Kudu maso Yamma ta Nijeriya da ya ziyarci Saudiyya domin gudanar da Umrah lokacin da waɗancan laifuka ke faruwa.
Waɗansu kuma masu yin sharhi akan lamarin daga nan gida Nijeriya sun gabatar da ra’ayoyin su kamar haka, “ya kamata Ƙasar Saudiyya ta yi hukunci ga duk wanda ya aikata irin wannan laifi, saboda bai dace a aikata haka ba a ƙasa mai tsarki.
“Kamata ya yi duk wani ɗan Nijeriya da yaje wata ƙasa daban, ya kwana da sanin cewar, wancan ƙasar tana da dokoki irin nata waɗanda ba su bai ɗaya dana Nijeriya ba. Kamata ya yi mutane su kiyaye ire-iren waɗannan abubuwa.”
Masharhantan waɗanda su ne Alhaji Bala Makwalla wanda ya yi sharhi na sama, Alhaji Ɗan Bala Ada, da Musa Maƙeri Kafin Madaki, dukkansu a garin Bauchi, sun kuma ce, “wanda duk ya yi mai kyau ya sani, kuma bai kamata a yi wasa da hukuma ko hukunci ba. Allah ya sa mu gane gaskiya.”
Musa Maƙeri Kafin Madaki shine mai faɗin “abinda ya dace shine a yi masu hukunci daidai da laifukan da suka aikata. Abubuwan da suka aikata ba ɗabi’a ce da ta dace ba. Allah kuma ya sa a yi masu adalci akan abubuwa da suka aikata.”