
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙasar Saudiyya ta fitar da sabon tsarin biza da zai shafi matafiya daga Nijeriya da wasu ƙasashe 13, wanda zai taƙaice masu zirga-zirgar shiga zuwa sau ɗaya a wata guda ba tare da zaɓin ƙari ba.
Hukumomi sun bayyana cewa bizar da ke bada damar shiga sau wani adadi a kan yi amfani da ita ta hanyoyin da ba su dace inda wasu ke amfani da ita wajen zama na tsawon lokaci da kuma yin aikin hajji ba a hukumance ba.
Hakan na zuwa ne bayan samun mahajjata 1,200 da suka rasa rayukansu a hajjin shekarar 2023 saboda tsananin zafi da cinkoso ya haifar, wanda hakan sa aka ga dacewar sauya tsarin bizar.
Saidai jami’an gwamnatin ƙasar sun ce dokar za ta yi aiki ne na wucin-gadi, inda gwamnati za ta kula da tasirin hukuncin gabannin ɗaukar mataki na gaba.