Saudiyya ta sako matan Nijeriya da ta tsare kan zargin safarar ƙwayoyi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin kasar Saudiyya ta wanke tare da sako mata ’yan Nijeriya uku da ta tsare su a lokacin aikin Hajjin shekarar 2024 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasarta.

Saudiyya ta sako matan ne bayan tattaunawar diflomasiyya tsakanin hukumomin ƙasashen biyu, a cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, Kimiebi Ebienfa.

A lokacin aikin Hajjin 2024 ne jami’an tsaron Saudiyya suka kama matan uku Hadiza Abba, Fatima Malah da Fatima Gamboi, da abin da ake zargin hodar Iblis ce, a Filin Jirgi na Yarima Mohammad bin Abdul Azeez da ke Madina.

Babban Jami’in Diflomasiyyan Nijeriya a Saudiyya, Ambasada Muazam Nayaya, ya ce, “Kama su na da alaƙa da wasu ’yan Nijeriya biyu da aka kama tun da farko ɗauke da kwayar hodar Iblis guda 80 da kuma guda 70.

“An kama matan ne kan zargin haɗa baki wajen taimakon da safarar miyagun ƙwayoyi da mutum biyun farkon ke yi,” a cewar ma’aitar, wadda ta bayyana cewa tsare su ya ɗauki hankali matuƙa a Saudiyya.

“An sako su ne bayan doguwar tattaunawar diflomsiyya da shari’a da suka kai ga wanke matan daga laifi da kuma sallamar su tare da mika su ga Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke birnin Jidda,” inji sanarwar.

“Ma’aikatar Harkokin Waje na son sanar da cewa ’yan Nijeriya uku, Hadiza Abba, Fatima Umate Malah, da Fatima Kannai Gamboi, an kama su tare da gurfanar da su gaban kotu bisa laifin safarar miyagun ƙwayoyi a ranar 5 ga Maris, 2024, a filin jirgin saman Yarima Mohammed bin Abdul Azeez International Airport Madinah, Saudi Arabia, an sake shi bayan shafe watanni 10 a tsare.

“Ma’aikatar tana son tunawa cewa kama mutanen uku ya ja hankalin Saudiyya da Niieriya sosai. An samu nasarar sako su ne bayan shafe tsawon lokaci suna hulɗar diflomasiyya da shari’a, wanda ya kai ga sallamarsu da kuma wanke su, da kuma mika su ga karamin ofishin jakadancin Nijeriya a Jedda.

“Matan sun samu tarba daga Ambasada Muazam Nayaya, ƙaramin jakadan Nijeriya a Jeddah kuma a halin yanzu suna jiran matakan shige da ficen da suka dace don dawowa Nijeriya don haduwa da iyalansu,” inji sanarwar.