Saudiyya za ta ƙara wa’adin yin biza ga ƙasashen da ke cikin dokar hana tafiye-tafiye

Daga AMINA YUSUF ALI

Ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa ta tsawaita wa’adin yin biza ga wasu ƙasashen da suke fuskantar dokar hana tafiye-tafiye. Inda ta tsawaita wa’adin har zuwa 30 ga watan Satumban bana. Kuma an ba su wannan dama ne ba tare da an caje su ko sisi ba.

Ministan hulɗa da ƙasashen waje na Saudiyya shi ya bayyana hakan a shafinsa na Tiwita. Ya ƙara a cewa, wannan dama ta tsawaita wa’adin bizar za ta yi aiki ne kawai ga mutanen da suka riga suka yi bizar shiga ƙasar ta Saudiyya amma kuma sai bizar ta su ta ƙare ba tare da sun shiga Saudiyya ba, sakamakon dokar hana tafiye-tafiye da ƙasashe suka saka saboda ɓullar annobar cutar Korona.

Harilayau dai, ya bayyana cewa, wannnan mataki ne da Ƙasar Saudiyya ta ɗauka a ƙoƙarinta na saita al’amuran ƙasar bayan tafiyar annobar cutar COVID-19. Sannan kuma da farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

Da ma tun a watan jiya ne hukumar samar da fasfo ta masar da ake kira ‘Jawazat’ ta fara tsawaita wa’adin takardar zaman ƙasa ga baƙi mazauna ƙasar (igama) waɗanda wa’adin igamar tasu ya cika. Sannan da kuma ‘yan ƙasar waɗanda wa’adin takardar izinin shiga ko fita daga ƙasar ya cika. Kuma duk an tsawaita musu wa’adin sabuntawa ba tare da biyan ko sisi ba.

Wannan doka ce da ta fito daga Sarkin Saudiyya Salman. Wanda ya bayyana cewa, wannan damar ba za ta shafi ‘yan ƙasashen waje wa]anda suke ɗauke da bizozin ƙasashe daban-daban ba. Haka a cewarsa masu ɗauke da bizar aiki da kuma bizar ziyara su ma ba za a bar su su shiga ƙasar ba, har sai sun je sun yi sati biyu a wani garin daban sun dawo, kana a ba su izinin shiga Saudiyya.

A yanzu haka ƙasashen da suke fuskantar dokar hana tafiye-tafiye sun ha]a da: Ƙasar Indiya, fakistan, Indunisiya, Misra, Turkiyya, Ajantina, Barazil, Afirka ta Kudu, Gamayyar Daular {asashen Larabawa, Itofiya, Bitnam, Afganistan, da labanan.