Saukar dala bai sauko da farashin kayan masarufi ba!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ana ta yayata bayanan yadda dala ta sauka a cikin makonni biyu da su ka wuce bayan mafi tsadar dalar a tarihi. Haƙiƙa tashin dala abu ne mai tada hankali tun da hakan kai tsaye na tafiya daidai da farashin kayan masarufi.

Abun damuwa ma shi ne in kayan su ka cilla sama ba sa saukowa sama-sam ko an samu saukar dalar. Ba mamaki ma a yi tunanin ai sai an sayar da kayan da a ke da su a lokacin tsada kafin a yi odar masu sauƙi.

Lamarin ba lalle ya zama haka ba don za a samu an odar kaya a na sayarwa sai a wayi gari an samu tashin farashin dala sai ka ga nan take farashi ya sauya ba tare da jiran sai tsohon kayan da ke hannu ya ƙare ba. Wani abun ma shi ne ba ma duk kayan ba ne a kan samu da amfani da dala don akwai kayan da daga farkon samar da su har shigar su shago a kasuwa bas a haɗuwa da dala.

A zahiri kenan a kan daga farashi ne da sunan dala don haka lalle sai an ɗauki wasu matakan na hana biyewa tashin dala ga tashin farashin kayan da mutane kan saya a kasuwa. Gwamnati da ’yan kasuwa ya dace su zama kan shafi ɗaya wajen hada-hadar kasuwanci. Idan har ba za a samu daidaiton farashin kayan masarufi ba, to ban ga ranar da talakawa za su daina hamma ko shiga tagayyara ba.

In an ce a koma noma don kasancewar san a duke tsohon ciniki, ba zai yiwu a sabon zamanin nan mutum ya duka a gonar da ta daɗe da tsufa ba ga shi ba taki sannan a cikata masa da cewa ya zama bawan damuna baturen rani. Abun nufi a nan za ka ji an ba da shawarar matuƙar mutane na son magance tsada kuma ta hakan su samu kuɗi to su koma gona don zai zama ba ruwan su da dalar birni.

Dazuka masu kwari da mutum zai iya nomawa ko ba wadataccen taki za ka taras ba sa shiguwa don barazanar tsaro. An samu labaran mutane da su ka tafi gona a ƙurgurmin daji a ka sace ko ma wasu hakan ya yi sanadiyyar ran su.

Sannan in gwamnati ta ce don taimakawa talakawa su yi noma ta kan ba da lamuni, ina ganin sai an yi kwakkwaran bincike don gano ko lamunin na shiga hannun manoman gaskiya ko kuwa a’a. Labaru ma na nuna wasu kan karɓi kuɗin da sunan noma amma sai su karkatar da su ta wani abun daban kamar gina sabbin ɗakuna, yin fenti a gida ko sayan babur ko mota da sauran su.

Ko ta ina a ka duba sai an fahimci lalle sai gwamnati ta zuba da sanya hannu wajen yin gyara da zai yi tasiri har mutane su gani a ƙasa. Idan gwamnati ta gyara dokoki za ta iya fahimtar yadda farashin muhimman kayan masarufi ya kamata su zama kuma duk wanda ya daga farashin ya dace a binciki dalili.

Kowace jiha ta na da ƙungiyar ’yan kasuwa kuma kowace kasuwa na da shugabanni. In ba za a gano yadda kasuwa ke karawa ko sarrafa farashi ba, to me amfanin ƙungiyoyin nan? Lalle sai gwamnati ta yi amfani da ma’aikatun kasuwanci da masana’antu wajen fahimtar yadda dala ke sa farashin kaya ya dage don hakan ya zama hanyar gyara ko daga vangaren ’yan kasuwar ko daga ɓangaren dokokin wasu hukumomin gwamnati da kan kawo cikas ga tafiyar kasuwanci ba ƙalubale.

Ya na da muhimmanci wannan tsari ya faro tun daga gwamnatin tarayya har zuwa jiha da can qananan hukumomi 774 na Nijeriya don ya shafi kowa kuma kowa ya samu kwanciyar hankali cewa gwamnati ta na yin abun da ya dace.

Duk kamfanonin da kan ƙera kaya a cikin gida ya dace a duba yadda a ke karɓar haraji daga wajen su don duba karawa ko sassauta harajin da hakan zai kawo tasiri a farashin kaya. Haka ma kayan da a kan shigo da su daga ketare ya dace a duba yadda hukumar kwastam kan karɓi haraji kan kayan don gano ko yawan harajin ke sa su dan karen tsada.

Sai gwamnati ta miƙe wajen zaukar duk matakan da su ka zama na ba sani ba sabo kafin samun gyara. Akwai manyan kamfanoni da kan ƙera kaya su kuma saka farashin da su ka ga dama kuma za ka ga ba abun da a ke yi mu su don haka a ke hasashen ko wasu shafaffu da mai ne a bayan fage ke mallakar kamfanonin don haka ba a taba su don kar ƙazamar ribar da su ke samu ta ragu.

A kan ma ji cewa an samu ragin farashi ne idan an samu muhawara ko rashin jituwa tsakanin manyan kamfanonin. Don jan hankalin masu saya sai ka ji kamfani kaza ya ce ya rage farashi amma a gaskiya ya kan iya zama don karya abokin gasar kamfanin ne a wani waje ko jiha sai ka ji an rage farashin kaza ko kaza.

Idan kowace jiha za ta tabbatar ta hada kan masu zuba jari su kafa kamfani mai amfani a jiha kamar yadda gwamnoni su ka yi gasar kafa filayen jiragen sama, da an samu sauƙi na kai tsaye. A qasar nan ne fa a ka ji shugaba Muhammadu Buhari na cewa hatta tsinken sakace haƙori daga ƙasar waje a ke shigo da shi.

Me zai hana a kafa irin waɗannan kamfanonin a cikin gida. Me zai hana a kafa kamfanin sarrafa fata wajen yin takalma ko jaka, me zai hana a kafa kamfanin yin garin madara daga madarar da a ke da ita a jihohi da dama.

A tsaunin Mambilla kadai za a iya cin gajiyar da adadi mai yawan a matasa za su samu ayyukan yi daga arzikin da ke jibge a yankin.

Sanennen bayani ne na masana tattalin arziki da ke cewa duk lokacin da ka ga qasa ta dogara da shigo da akasarin kayan da ke buƙata daga ketare to ba yadda darajar kuɗin ta zai zauna.

Wani abun damuwa ma shi ne na ɗanyen man fetur da Nijeriya ke fitarwa ketare don sayarwa amma sai ta sayo tatacce daga ketare da kan sa lalle sai an zuba tallafi matukar za a sha man da araha.

Kun ga da ya dace a ce ƙasar na da matatun man fetur kamar ƙasashen ƙetaren da kan tace a shigo da shi da dan karen tsada. An sha yin alwashin gyara matatun amma ina shiru ka ke ji wai Malam ya ci shirwa.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijeriya EFCC ta ba da belin ɗan canjin kuɗi a kasuwar canji ta Abuja Muhammad Adam Almustapha da a ka fi sani da Mustapha Naira bayan buƙatar hakan daga dattawan kasuwar canjin da su ka jajirce sai sun karvo abokin kasuwancin na su.

EFCC dai ta kama Mustapha Naira bisa zargin ya furta kalaman da ke neman tada farashin dala a daidai lokacin da Naira ta samu koma bayan da ba ta tava samu ba a tarihi. Hakanan Naira ya zargi hukumar EFCC da dirar mikiya kan ’yan canjin don yawancinsu Hausawa ne da a kan ambace su da kalmar ABOKI don rainin wayo.

Samame a kasuwar canjin ya haddasa sanya wasu ’yan kasuwar buya inda har ta kai ga EFCC ta kama wasu daga cikin ’yan kasuwar amma daga bisani ta sake su.

Gabanin yayata wani labarin marar tushe da ke cewa Amurka ma ta shirya canja kuɗi da daina karvar takardar da a ka buga kafin 2021, kasuwar canjin ta tumbatsa da masu sayen dala don boye maqudan kuɗinsu na Naira da gujewa zuwa banki kar su fada tuhuma daga EFCC; hakan ya cilla dala har fiye da Naira 900.

Tsohon shugaban kasuwar canjin Alhaji Salisu Garu na daga waɗanda su ka karɓo belin Mustapha Naira wanda EFCC ke son gani lokaci-lokaci kafain shafa ma sa lafiya. Garu ya ce za su cigaba da bin ƙa’ida don tashin dala yanayin kasuwa ke kawo shi amma ba lalle ’yan canji ke haddasa matsalar ba.

Sakataren kwamitin dattawan kasuwar canjin Alhaji Yahaya Jidda Kida ya ce ba sa zagon ƙasa ga tattalin arziki kuma su na mara baya ga sauya fasalin kuɗi amma ya na da kyau a yi la’akari da al’ummar karkara.

Dalar dai ta fara murmurewa daga faɗowa da ta yi da kusan Naira 25; kazalika dalar ba ta samuwa yanda a ka saba a bankuna sai an yi ta jeka-ka-dawo.

Kammalawa;

Duk maufofi da tsare-tsare da gwamnati za ta ɓullo da su to ta yi haka don rage tasirin tashin dala kan tasirin tashin farashin kayan masarufi. Ko talakan talak ba zai iya cin tuwo da miya mai nama ba, to aƙalla ya samu tuwon ko na dawa ne da miya mai wake.

Abun da kan kawo tsama a tsakanin talakawa da masu hannu da shuni shi ne rashin buɗa wa talakawa hanyar da za su samu abu daidai ƙarfinsu. Idan har talakawa ba za su iya sayen kwanon masara ba yayin da masu kuɗi ke shan inabi da gutsurar tuffa, ai zaman lafiya zai yi wuyar samuwa.