Saura ƙiris a bai wa hamata iska a tskanin jami’an gwamnati kan Abdulrasheed Maina

Daga BASHIR ISAH

An samu ‘yar ƙwarya-ƙwaryar wasan kwaikwayo a harabar Babbar Kotun Abuja tsakanin jami’an kula da gidan yari da na EFCC bayan da kotun ta yanke wa tsohon shugaban kwamitin yi wa fansho garambawul ko kuma PRTT a taƙaice, Abdulrasheed Maina hukuncin zaman gidan yari na shekaru takwas.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, Alƙali Okon Abang shi ne wanda ya yanke hukuncin ingiza ƙeyar Maina zuwa gidan yari bayan da hukumar EFCC ta maka shi a kotu bisa tuhumar badaƙalar kuɗaɗe.

Alƙali Abang ya bada umarnin Maina zai soma zaman kurku na duka laifuka 12 da aka kotu ta kama shi da su daga ranar 25 ga 2019, wadda ita ce ranar da aka gurfanar da Maina a kotun.

Kazalika, hukuncin da aka yanke wa Maina ya haɗa da maido da maƙudan nairori sama da biliyan guda zuwa asusun Gwamnantin Tarayya. Haka nan, hukuncin ya shafi kamfanonin da aka yi amfani da su wajen tafka maguɗin kuɗaɗen.

Sai dai an samu tsaiko a daidai lokacin da jami’an EFCC suka nemi yin wuf da Maina a harabar kotun, inda suka shigo harabar kotun da motoci biyu suka tare gaban motar gidan yarin da a cikinta aka shirya ɗaukar Maina zuwa gidan yari na Kuje.

Wannan al’amari ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin jami’an gidan yari da na EFCC wanda har ya kai ga kowane ɓangare ya gyara zaman bindigarsa don shirin harbi.

Majiyar NAN ta ce jami’an EFCC sun shigo harabar kotun ne don su sake kama Maina bisa zargin wasu laifuka na daban. Har ma da cewa suna da izinin kamu (warran arrest) don sake cafke Maina wanda aka yanke masa hukuncin zaman kaso na tsawon shekaru 12 ba da jimawa ba.

An ce jami’an gidan yari sun ce huruminsu ne tafiya da Maina tun da kotu ta riga da ta yanke masa hukunci, amma idan har jami’an EFCC ɗin na da buƙatar sake kama shi “sai su bi ta hannun kotu, kotun za ta ba mu umarnin da za mu bi”, in ji majiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *