Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Sakkwato ta Kudu Honarabul Ya’u Muhammad Danɗa ya bayyana cewa sauran ƙabilu da ba ‘yan asalin jihar Sakkwato ba su ma za su ci moriyar dimokuraɗiyya a yankin.
Ya bayyana haka ne ranar Talatar da ta gabata yayin da ƙungiyar Yarbawa mazauna yankin ƙaramar hukumar mulki ta Sakkwato ta Kudu suka kai masa ziyarar jaddada goyon bayansu ga Jam’iyyar APC.
Ya bayyana cewa bisa ga irin horon da suka samu ga iyayen gidansu na siyasa ba za su manta da duk wanda ya bayar da gudummawa wajen ganin sun samu nasara ba. “Muna sane da irin rawar da kuka taka tun lokacin yaƙin neman zaɓe har zuwa lokacin zaɓen saboda haka ba wani bambanci da za mu nuna muku, kuma za ku ci moriyar dimokuradiyya kamar yadda yayan asalin jihar za su ci,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “In Sha Allahu duk lokacin da aka soma waɗansu shirye-shirye musamman abinda ya shafi tallafin jari, koyar da sana’o’i ga mata da matasa dadai sauransu ba za a bar su a baya ba saboda tun kafin siyasa mun sani muna tare da ku.”
Tun farko da ya jawabi, shugaban tawagar Alhaji Salman Muhammed Oke kuma shugaban al’ummar Yarbawa a karkashin Jam’iyyar APC ya bayyana cewa sun zo ne don taya shi murnar lashe zaɓe da kuma jaddada goyon bayan su ga Jam’iyyar APC da kuma jagorancinsa.
Ya bayyana cewa bayan wannan kuma kamar yadda suka taso a tafiya tare za su cigaba da bayarda gudummawa ga Jam’iyyar APC da kuma jagorancin ta.
Ya yi kira ga shugaban da ya mika koken su musamman wajen gwamna Ahmed Aliyu Sokoto da kuma jagoran siyasar arewacin Nijeriya Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da idan aka soma shirye-shiryen tallafi kamar yadda aka saba don Allah kada a manta da su saboda su ma su ci moriyar dimokuraɗiyya.
Ya kuma bayyana cewa su fa ba su ɗauki kawunansu a matsayin baki ba saboda a Sokoto saboda ba su taba samun wata tsangwama ba.