Sauraren Ƙararrakin Zaɓe: Atiku Abubakar ya halarci zaman kotu

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya halarci zaman shari’ar da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe ki yi a Abuja a wannan Alhamis ɗin.

Atiku ya halarci Kotun ne domin jin yadda za ta kaya kan ƙarar da ya shigar inda yake ƙalubalantar nasarar da ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya samu a babban zaɓen da ya gudana.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar shi ne ya zo na biyu a babban zaɓen da aka yi ran 25 ga Fabrairu, yayin da Peter Obi na Jam’iyyar Labour ya zo na uku.

Atiku yana zargin an tafka maguɗi a zaɓen wanda hakan ya sa aka bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Haka shi ma ɗan takarar Jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya halarci zaman da Kotun ta yi a farkon wannan makon don sauraren shari’a kan ƙarar da ya shigar ta ƙalubalantar sakamakon babban zaɓen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *