Sauyin sheƙa ko rashin kunya?

Daga AUWAL GARBA ƊAN BORNO

A jihar Kano, bayan sanar da Abba Kabir Yusuf a Matsayin Wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Kano na 2013.

Abubuwan sun ta faruwa, na mamaki al’ajabi da kuma wani Abu da ya yi kama da rashin kunya.

Babu laifi ga ɗan jam’iyyar adawa ya fito fili ya taya wanda ya lashe zaɓe murna, haka babu laifi ga ɗan adawa ya karɓi ƙaddara ya yi wa Wanda aka sanar fatan Alheri da kuma addu’a ta samun nasara a mulkinsa.

Amma a yi yaƙi da kai a wani ɓangaren. Ɓangaren da ka yaƙa ya samu nasara, ba kunya ba tsoron Allah, a daren da aka sanar da nasarar ka yi caraf ka koma vangaren da suka yi nasarar. Wannan ya zama rashin kunya da rashin lissafi da kuma raina tunanin waɗanda ka koma wajensu. A ɓangaren wadanda ka bari kuma ya zama cin amana da rashin dattako.

Akwai ‘Yan Siyasar da duk yadda juyi ya juya za a juya da su. Irin waɗannan ‘yan siyasar kafin su sauya sheƙa, sukan jira wata gava, ana samun dama, za su yi amfani da wannan damar su sauya sheka zuwa sabuwar gwamnatin da ta ci nasara. Su kuma su Malam Abba Musa ganin da su aka yi yaƙin suna ganin fa yanzu su ke da gwamnati. Abinda ba su sani ba, duk lokacin da aka kafa sabuwar gwamnati, akwai waɗanda ba a yi aikin kafin da su ba, kuma su za su zama na gaba-gaba a wajen damun furar da kamun ludayin.

Watarana muna Kaduna tare da wani babban ɗan kwangila a Gwamnatin Lamaran Yero. Ana tsaka da kamfen na tazarcensa, sai wani ɗan adawa ya shigo yake zolayar mutumin da muke tare da shi, cewa sai sun ka da su da Yardar Allah. Sai. Ya ba shi amsa da cewa ai mu ko Fir’auna ne zai zama gwamnan Kaduna da mu za a ci.

Roƙon da ɗan adawa ya yi ya amsu, bayan zaɓe aka kayar da Gwamnatin Lamaran Yero. Shi ma ɗan kwangila maganarsa ta tabbata, bayan an fara mulki a sabuwar Gwamnati na samu labarin ya fara Kwangiloli. Ba wani abun Mamaki ba ne bayan kafuwar Gwamnatin Gida-gida, ka ga su Auwal Philosoper, Adamu Maikudi Aminu, Rabiu West a sahun gaba wajen raba takardar Gurbin Karatu a ƙasar waje.

Auwal Danborno, Marubuci ne, kuma ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto daga Kano.