Sayayya 10 mafi tsada a tarihin ƙwallon ƙafa

A halin yanzu, yayin da duniya ke jiran a tabbatar da cinikin Paul Pogba wanda zai kama kusan fam miliyan £100 daga Juventus zuwa Man Utd, idan hakan ta tabbata, to zai zama sayayyan da ya fi kowane tsada a duniya.

Blueprint Manhaja ta kawo maku sauran sayayyen da su ka fi kowane tsada a duniya. Ban da shahararru irin su Cristiano Ronaldo da Bale da aka sani, akwai wasu hala waɗanda ba a sani ba. Ga dai jerin ’yan wasa 10 nan, waɗanda cinikin su ya fi na kowa tsada a duniya.

Ƙungiyar Man City, wanda ta yi ƙaurin suna wajen ɓarnar kuɗi ta sayo ɗan wasa, wanda ko a shekarar da ta gabata ta kashe maƙudan kuɗi har fam miliyan £55 wajen sayo ɗan wasa daga Wolfsburg. Ɗan wasan na tsakiya ainihin ɗan Ƙasar Belgium ne.

Ɗan wasan duniya na Shekarar 2007, Ricardo Kaka ya bar AC Milan ta Italiya zuwa Real Madrid shekarar 2009 kan kuɗi fam miliyan £56.

A ranar da aka sayi ɗan wasa Zlatan, an saida rigunan sa sama da 80,000. Ɗan wasan na ƙasar Sweden ya shiga tarihi ne lokacin da Barcelona ta sayo sa daga Inter Milan kan kuɗi fam miliyan £56 a shekarar 2009. A cinikin Barcelona ta haɗa da ɗan wasan ta Samuel Eto’.

Cinikin Di Maria ne wanda ya fi kowane tsada a ƙasar Birtaniya. Man Utd ta bada kuɗi har fam miliyan £59.7 ga Real Madrid a shekarar 2014. Sai dai bayan shekara ɗaya rak, ɗan wasan ya ƙara gaba.

Bayan ɗan wasa James ya nuna kan sa a World Cup, tuni ƙungiyar Real Madrid ta sayo ɗan wasan na Ƙasar Colombia kan kuɗi miliyan £63 daga ƙungiyar Monaco.

Tauraron Ƙasar Brazil, Neymar ya ci ma Bareclona aƙalla fam miliyan £71.5, an sayo sa ne daga ƙungiyar Santos da ke Brazil bayan an ɗauki dogon lokaci ana ta raɗe-raɗi.

Ba za a manta da Suarez ba ko ɗan gartsawa jama’a cizon da ya saba. Haka Barcelona ta lale kuɗi har fam miliyan £75 ta saye ɗan wasan na Ƙasar Uruguay daga Liverpool.

Tsohon ɗan wasan gaba na ƙungiyar Real Madrid Higuain, ya koma Juventus da Ƙungiyar Napoli kwanaki kaɗan da suka wuce kan kuɗi miliyan £75.3. Higuain ya karya wani tarihi da aka kafa tun shekaru 66 da suka wuce baya.

Ɗan wasan da ya fi kowa tsada a duniya kenan kafin shekarar 2013, Man Utd ta saida Ronaldo zuwa Real Madrid kan kuɗin da ba a taɓa ganin irin su ba a wancan lokaci, fa miliyan £83.7 a shekarar 2009. Yanzu dai haka kaf tarihin kulob ɗin na Real Madrid babu wanda ya taɓa cin ƙwallaye kamar Cristiano, kuma yana kan ci har gobe.

Ɗan wasa Bale na Ƙasar Wales shine ɗan wasan da ya fi kowa tsada a duniya. Ƙungiyar Real Madrid ta kashe fam miliyan £93.1 wajen sayen ɗan wasan daga Tottenham shekaru uku da suka wuce. Kawo yanzu, Bale ya ci kofin Uefa Champions League biyu a zaman san a Real Madrid.