Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Sha’awar ganin an sauya mummunan kallon da wasu daga cikin al’umma ke yi wa masu maganin gargajiya ce ta sa Wazirin Maganin Jihar Kano, Alhaji Nasiru Sani Abubakar, ya sadaukar da dukiyarsa wajen ɗaukar nauyin horar da masu maganin gargajiya domin ƙara musu ilimi da ƙwarewa a sana’arsu.
Wazirin Maganin, wanda kuma shi ne Shugaban ƙungiyar Masu Maganin Gargajiya ta “Moden” da “ƙAA” na masu maganin gargajiya, Alhaji Nasiru Sani Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan kammala bitar kwanaki shida da aka shirya wa ƙwararrun masu maganin gargajiya 60 a Jihar Kano.
An gudanar da bitar ne ƙarƙashin ɗaukar nauyin kamfaninsa na Shafa’u Linnas Habal International, inda aka horar da mahalarta kan wasu hanyoyin zamani da za su taimaka wajen inganta sana’ar maganin gargajiya.
Da yake jawabi, Alhaji Nasiru ya ce bitar ta yi tasiri matuƙa, domin dukkan waɗanda suka amfana da ita sun nuna farin ciki tare da fahimtar abubuwan da aka koya musu cikin sauri, duk da cewa su ƙwararru ne a sana’ar.
“Wannan bita da aka yi, mutane za su yi mamaki nan gaba. Duk wani kallo da ake yi wa masu maganin gargajiya zai canza, za a ƙara samun amincewa da su sosai,” inji shi.
Wazirin Maganin ya yi kira ga ’yan uwansa masu maganin gargajiya da su ji tsoron Allah tare da tsaftace wannan sana’a da ya bayyana a matsayin mai asali da muhimmanci.
Ya ce jama’a sun ba masu maganin gargajiya amana, don haka bai kamata su ci amanar wannan amana ta hanyar cutar da mutane ko gallaza musu ba.
Ya kuma yi kira na musamman ga masu yawo suna tallan magunguna da amsa kuwwa mai ƙarfi, musamman waɗanda ke tafiya tare da ƙananan yara, suna shiga lungu da saƙo ba tare da kula da lokutan Sallah ko lokacin da mutane ke barci ba. Ya ce irin wannan ɗabi’a ba ta dace ba.
Wazirin Maganin Jihar Kano ya kuma ja hankalin waɗanda suka samu horon da kada su yi sakaci da ilimin da suka samu, yana mai cewa ya kamata su yi amfani da shi wajen inganta sana’arsu.
“Sun ga yadda muka wahala muka yi wannan aiki ba dare ba rana. Mun yi shi ne saboda mun san muhimmancinsa. Lallai su riƙe wannan karatu, ya zama linzami a duk inda suka zauna wajen gabatar da sana’arsu,” inji shi.
A nasa ɓangaren, Shugaban Makarantar Maganin Gargajiya ta Afirka, MIJ College, Farfesa Muhammad Ibrahim Jawa, ya bayyana cewa bitar ta kwanaki shida ta ba shi mamaki, tare da tabbatar masa da cewa abin da ake son masu maganin gargajiya su zama a ƙasar nan, za a iya cimma shi.
Ya yaba da yadda mahalarta bitar suka riƙa zuwa akan lokaci tare da bin duk ƙa’idojin da aka gindaya domin gudanar da bitar.
Farfesa Jawa ya ce tun farko ba a shirya gudanar da bitar a Kano ba, amma saboda kishin Wazirin Maganin ne aka kawo ta jihar domin bai wa masu maganin gargajiya damar amfana da ita.
Ya ƙara da cewa, “Tun da na kafa wannan makaranta shekaru 10 da suka gabata, babu mutum ɗaya da ya taɓa ɗaukar ɗimbin kuɗi ya biya wa mutane masu sana’a tare da shi, ba ’yan uwansa ba, ba mutanen garinsu ba, saboda kawai inganta sana’a sai Waziri. Ban ga kamarsa ba. Allah ya saka masa da alheri, ya yi matuƙar ƙoƙari,” inji Farfesa Jawa.
Farfesa Muhammad Ibrahim Jawa ya yi kira ga waɗanda suka amfana da bitar da su yi aiki da abubuwan da suka koya, domin cimma manufar da aka shirya horon a kanta.
Ya kuma gode wa dukkan waɗanda suka bayar da gudummawa wajen ganin an samu nasarar bitar, musamman waɗanda suka sadaukar da lokacinsu suka je Kaduna domin samun ƙarin ilimi, daga bisani suka dawo domin koyar da ’yan uwansu.
Ya yi addu’ar Allah ya saka wa dukkan waɗanda suka taimaka wajen ganin an gudanar da bitar cikin nasara da alheri.
Shi ma a nasa ɓangaren, Sarkin Shimfiɗa na Maganin Gargajiya na Jihar Kano, Alhaji Sani Muhammad Tsamiya Babbar, ya yaba da kyakkyawar niyyar Wazirin Maganin, bisa wannan dama da ya samar domin masu maganin gargajiya su ƙara samun ƙwarewa da ilimin zamani.
Ya kuma gode wa Farfesa Muhammad Ibrahim Jawa bisa kawo musu wannan dama ta samun ƙarin ƙwarewa da koyon sabbin hanyoyi na zamani domin kyautata da bunƙasa sana’ar maganin gargajiya.
A ƙarshe, ƙwararrun masu maganin gargajiya 60 da suka samu horon sun kammala bitar cikin nasara, inda aka bayyana fatan cewa za su yi amfani da ilimin da suka samu wajen inganta ayyukansu da kuma ƙara amincewar al’umma da sana’ar maganin gargajiya.
