Shahara da karɓuwa ce babbar nasarar kowanne jarumi – Baba Ɗan Audu

Daga AISHA ASAS

A kowacce irin sana’a da mutum zai yi, yakan yi fatan samun nasara da kuma ɗaukaka, kamar yadda masu azancin magana ke cewa, “ka nemi sa’a ba iyawa ba, domin sa’a ta fi iyawa.” Da wannan ne ake samun wasu su fi wasu a harkokin da suka sa a gaba.

Da yawa sun fahimci nasara daga Allah ce, duk ƙoƙarinka za ka iya tarar da wanda bai fi ka ba ya zama sama da kai, wannan ne ke taimako wurin yaƙar shaiɗan wurin hana shi sanya ma ka hassadar waɗanda suka fi ka.

Hakazalika, akan samu wasu da suka haɗa biyun, wato iyawa da kuma sa’ar, wanda hakan ke sa a amince da sun cancanci duk wata ɗaukaka da suka samu.

Rabi’u Rikadawa wanda a yanzu aka fi sani da Baba Ɗan Audu, jarumi ne da ya cancanci a kira da gwani a fagen wasan kwaikwayo, kuma mutum ne da za mu iya cewa Allah Ya albarkaci abinda yake yi, kasancewar ya ɗaukaka shi, Ya ɗaga shi a idon duniya, har ya zama a layin farko da masana’antar finafinai ta Kannywood ke ji da alfari da su.

Da wannan ne jaridar Blueprint ta tattauna da shi, don cika alƙawarin da muka ɗaukar ma ku, na kawo ababen da makarantanmu za su gamsu da shi. Idan kun shirya, sai in ce a sha karatu lafiya:

MANHAJA: Sunanka a bakunan mutane ya zama abin faɗa a ɗan wannan lokaci, sakamakon rawar da ka ke takawa a shiri mai dogon zango na ‘Labarina’ a matsayin Baba Ɗan Audu. Me za ka ce game da wannan nasarar?

BABA ƊAN AUDU: To, ba abinda zan iya cewa, sai godiya da zan miqa ga mahaliccina. A matsayina na ɗan-adam Ina yin iya yina ne kawai, ba tare da tunanin zai kai inda na kai ba. yanayin yadda mutane suka karɓi wannan aikin nawa, wani lamari ne daga ubangiji, domin alamu ne na sun fahimce abin yadda ya kamata, don haka babu inda zan kai godiya ta sai wurin Allah.

Magana ta gaskiya, ba yi na ba ne, ban yi wani yunƙuri na ganin wai na samu karvuwa ga mutane ba kan aikin, kawai dai na yi abinda na fahimta game da rawar da ake so in taka.

Kamar misalin mai siyar da abinci ne a kasuwa, lokacin da ya je zai tarar da akwai wasu da ke kasuwancin irin abincin a wurin, amma sai ki ga nasara ta ziyarce shi, nasa abincin ya ɗara na saura karvuwa. Kinga kuwa ba dabarunka ne ya ba ka wannan nasara ba, hukunci ne na Allah, Shi Ya ce ka zamo kuma ka zamo. Duk da hakan zan miƙa godiya ga masu kallo da suke yaba wanna aikin da na yi, kuma Ina mai tabbatar masu, zan ƙara zage damtse, na ƙara daga irin abinda nake yi, don ganin na ci gaba da ba wa masu kallo abinda suke so.

Ko ka fuskanci wata matsala yayin da ka ke rikiɗewa izuwa Baba Ɗan Audu?

To, zan iya cewa na ɗan samu ‘yan ƙalubale kan hakan, amma Allah cikin ikonSa na samu nasarar kwankwaɗe su, suka zama tarihi. Dama ni a duk lokacin da aka ba ni rol ɗin da zan hawa, na kan yi dogon nazari kansa, ta yadda zan iya fahimtar sa sosai, wanda hakan zai ba ni damar yin ƙoƙarin kutsa raha a ciki, hakan kuma zai taimaka ƙwarai wurin bayar da hankali ga fahimtar saƙon da ake so a isa. Wannan kuma wata baiwa ce da ba kowanne jarumi ne aka hore wa ba.

Me za ka ce game da ɗimbin nasarar da ka samu?

Ba abinda zan ce sai alhamdu lilla. Dama babbar nasarar kowanne jarumi ita ce, ya samu shuhura da karɓuwa daga wurin masu kallo. Ko da kana da iyawa ko fahimtar harkar, a matsayinka na jarumi, idan har ba ka samu karɓuwa ba, aikinka zai zama na banza kenan.

Abin godiya shi ne, yadda rol ɗin da na taka ya samu karɓuwa, wanda hakan ya kai ni ga kamfanoni da dama suna nema na don yin tallace-tallacen su. Kuma wani abin birgewa kuwa, musamman suke bayyana Baba ɗan Audu suke nema ga aikin. Wanna zai ƙara bayyana muhimmancin samun karɓuwa a harkar fim, ga shi ainahin shirin fim ɗin da aka yi da kuma cigaban jarumin da ya yi.

Idan mun koma baya a rayuwarka a harkar fim, a baya an san ka ne a matsayin Dila, sai dai zuwan Baba Ɗan Audu ya turbuɗe wannan sunan. Ya za ka iya kwatanta tsakanin sunayen biyu?

Shi dai sunan suna ne da na samu a masana’antar fim, kuma shi ma Baba Ɗan Audu, kaga kuwa dukkansu gida ɗaya suka fito, don mutane suka sa min, albarkacin harkar fim. Dila ya samo asali ne a wani fim da na yi shekaru masu yawa da suka wuce. Duk da jimawar shekarun har yanzu Ina samun masu kira na da sunan, kuma Ina amsa masu.

Abinda ya fi komai ba ni mamaki game da wannan suna na Dila shi ne, duk da kasancewar sa tsohon suna da ya jima, na kan ci karo da yara masu kira na da sunan. Sun koyi sunan ne daga iyayensu. Ba zan manta ba ko a baya-bayan nan, kusan kammala yaqin neman zaɓen Jihar Kaduna, 2023, na Jam’iyyar APC, an gabatar da ni da sunana, Rabi’u Rikadawa (Baba Ɗan Audu) amma sai da wani daga ciki ya ce, “ni dai na sanka ne a matsayin Dila, ba Baba Ɗan Audu ba.” kinga kuwa har yanzu akwai masoyan Dila.

Daga ƙarshe, wane saƙo ka ke da shi ga masoyanka?

Saƙona ga masoyana dai shi ne, Ina son su sosai, fiye ma da yadda suke sona. Kuma a kullum Ina ƙara jadadda cewa, duk wata ɗaukaka da ka samu, haqiqa yi ne na Allah. Domin ba don amincewar ubangiji ba, duk jimawa da ƙoƙarin da za ka yi a masana’antar ba zai ba ka ɗimbin masoya ba. don haka Ina mai ƙara tabbatarwa masoyana Ina alfahari da su sosai.

Mun gode.

Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *