Shahararren ɗan bindiga, Kachalla Ɗan Lukuti, ya mutu yana haushin kare

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani shahararren ɗan bindiga mai suna Kachalla Ɗan Lukuti, wanda ya addabi al’ummar Jihar Zamfara, ya mutu a wani yanayi mai ban mamaki.

A cewar Zagazola Makama, wani masani kan yaƙi da tada ƙayar baya a yankin Tafkin Chadi, ɗan ta’addar, wanda ya yi ƙaurin suna wajen kitsa munanan hare-hare a jihohin Zamfara da Katsina, ya mutu ne bayan ya yi fama da wata rashin lafiya da ba a saba gani ba, wacce ta sa shi yin haushi kamar kare kafin rasuwar tasa.

Zagazola ya ce, ɗan Lukuti ya kamu da rashin lafiya kusan mako guda da ya gabata, inda ya samu wasu alamu da suka haɗa da amai da kuma ci gaba da yin haushi da ke kama da na kare.

Ya ce, ’yan ƙungiyarsa ba su samu damar zuwa wajensa ba, saboda yadda halin da yake ciki ya kasance mai ban mamaki, lamarin da ya tilasta musu zama daga nesa har sai da ya mutu.

ɗan Lukuti ya kasance shugaban ‘yan bindiga da ake fargabar yana aiki daga dajin Kokonba da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Ya umurci ‘yan bindiga sama da 50, kuma shi ne ke da alhakin kai hare-hare da dama a garuruwan ɗan Jiloga, Rijiya, Zonai, Magami, da kan babbar hanyar Gusau zuwa Magami, inda ya ƙara kai hare-hare a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Duk da ta’addancin da ya yi, lokacinsa na ƙarshe ya sha wahala da ba za a iya misaltawa ba, kamar yadda shaidun gani da ido suka ruwaito cewa ya yi ƙururuwa da kuka har ya mutu.

’Yan ƙungiyarsa, saboda tsoro da camfe-camfe, sun tilasta wa mutanen ƙauyen Kizara gudanar da jana’izarsa, inda suka kwantar da shi a makarantar firamare ta yankin.

An yi imanin cewa mutuwarsa mai ban mamaki na iya kasancewa yana da alaƙa da cutar karnuka ko kuma sakamakon ruhaniya na shekarunsa na ta’addanci.

Mutuwar tasa ta biyo bayan tsauraran hare-haren da sojoji suka kai a yankunan ‘yan bindiga a faɗin Arewa maso Yamma.

A wani labarin kuma, Karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina ta gudanar da taro karo na biyu da nufin samar da zaman lafiya tsakanin jami’an tsaro, mazauna yankin da kuma ‘yan ta’addan da ke addabar yankin, a kokarin kawo karshen hare-haren da suke kai wa.

A cewar wata majiya da ta shaida taron kuma ta zanta da gidan rediyon Alfijir, tattaunawar ta hada da manyan shugabannin ƙungiyoyin da suka dade suna addabar yankin.

Majiyar, wacce ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ƙara da cewa, “’yan bindigar sun kai ɗari-ɗari a lokacin da suka halarci taron sulhun.