Shaikh Zakzaky a shekaru 70 masu albarka

Shaikh Zakzaky

Daga NAJEEB MAIGATARI

A shekarar 2009 an gayyaci Chimamanda Ngozi Ndichie zuwa wani taro da ‘TED talk’ ta shirya a jami’ar Oxford da ke birnin Ingila. Cikin muƙalar da ta gabatar a taron mai taken “The Danger Of A Single Story” ta bayyana hadarin da ke tattare da labari daya tilo mai bangare daya (single story).

Cikin jawabin ta a lokacin, Chimamanda ta bayyana irin tasirin da ‘single story’ ya ke da shi ga al’umma, ta yanda cikin ƙanƙanin lokaci ake yarda da wannan labarin, ko da ya saba da abun da ya ke a zahiri. Misali, saboda yanda marubuta a ƙasashen Turai ke bayyana nahiyar Afrika ya sanya mafi yawan turawa (wadanda su ka karanta irin wannan labarin) ke tunanin kowane dan Afrika ya na rayuwa ne cikin talauci, cututtuka, da kuma tsananin yunwa. Kamar yanda ya shahara a cikin al’ummar mu cewa duk wanda ke kokarin wayar da kan al’umma akan yawan haihuwa barkatai, to dan aiken yahudawa ne.

Haɗarin da ke tattare da maimaita labari ɗaya tilo (single story) akan wani mutum, ƙasa, nahiya ko wata mas’ala shi ne ya na mayar da wannan labarin da ake fada ya zama shi kaɗai ne labarin da aka sani, kuma aka yarda da shi; a yayin da a lokaci guda kuma ya ke tauye haƙƙi da kuma nuna wanda/abun da ake yada labarin akan shi da wata siffa ta daban wacce ta saba da haƙiƙar sa.

Wannan muƙala ta Chimamanda Ngozi ta dace sosai da yanda ake fassara rayuwar jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Shaikh Ibrahim Zakzaky (H)- ko da yake shi ba labari ɗaya ne aka ƙirƙira akan shi ba, su na da yawa sai dai kowanne daga ciki yana ɗaukan ma’anar irin ‘single story’ din da Chimamanda ta bayyana haɗarin shi.

Mafi yawan mutane, tun tasowa a yarinta, ana ta maimaita mu su labari daya tilo (single story) mai fuska ɗaya akan Shaikh Zakzaky (H)- wanda kuma hakan ya haifar da akasarin su ke daukan shi sabanin yanda ya ke a zahiri.

Daga cikin irin labaran da ake yaɗawa akan shi (wanda ya zama ruwan dare) shi ne: Shaikh Zakzaky (H) ‘bai yi karatu ba’ ya tara jahilai su na biye da shi, kuma mutum ne marar son zama lafiya; akan su ne kuma zan yi ƙarin haske. Akwai batun cewa ya na son kafa daular shi’anci a Najeriya irin wacce Ayatullah Khumaini (Q) ya kafa a ƙasar Iran (wannan wani maudu’i ne da ya ke buƙatar yin rubutu na daban akan shi).

A yau idan za a tambaya cikin yara da manya, mata da maza, tsofaffi da matasa: wanene Shaikh Zakzaky (H)? Mafi yawa amsar da za su bada za ta dace ne da wancan ‘single story’ da ake yaɗawa akan shi. Ƙalilan daga ciki ne, waɗanda su ka bincika gaskiya, za su fadi haƙiƙanin yanda Shaikh ɗin ya ke.

Da gaske ne Shaikh Zakzaky (H) bai yi karatu ba, kamar yanda wancan ‘single story’’ din ya bayyana shi? A cikin wata hirar da ya yi da jaridar Daily Trust a shekarar 2016, Malam Sani Yakub (dan uwan Shaikh Zakzaky na jini), duk da irin adawar da ke tsakanin shi da Shaikh Zakzaky (wanda ke da alaqa da ‘yan ubanci da kuma aƙidanci) ya bayyana cewa: “Ibrahim haziƙin yaro, mai tsananin kaifin basira da fahimtar karatu. Mun yi karatu tare da shi kuma ya kasance yana riga mu haddace karatu”.

Wannan ke nuni da cewa Shaikh Zakzaky (H) tun tasowar sa karatu ya sanya a gaba, farko a gurin mahaifin sa (Allah Ya yi masa rahama), daga baya kuma a gaban wasu fitattun Malamai kamar marigayi Malam Isa Waziri Kano, Malam Shawish Abdallah Kano, Malam Sani Abdulƙadir Zariya, Malam Ibrahim Kakaki, Malam Abdallah Sagagi, Malam Nuhu (limamin Yola), da sauran su.

Kasancewar sa ɗalibin Malam Shawish, hakan ya ba shi damar halartar wasu karatuttukan fitaccen malami masanin Allah, marigayi Malam Nasir Kabara (R). A ɓangaren karatun zamani (boko) kuwa, ya kasance fitaccen ɗalibi a sashen tsimi da tattalin arziƙi (economics) a jami’ar Ahmadu Bello da ke garin Zariya.

Daga cikin mabiyan shi akwai manyan malamai, fitattun masana. Wasu har yanzu suna tare da shi, wasu kuma kamar su Dr. Bashir Aliyu Umar, Prof. Mansur Sokoto sun bar shi daga baya (saboda bambancin mazhaba). Har wala yau, daga cikin mabiyan shi akwai Farfesosi da Daktoci, Likitoci, Injiniyoyi, Lauyoyi, da sauran masana a fannonin Ilimi daban-daban. Yaushe kuma za’a danganta mabiyan shi da jahilci?

Dangane da batun rashin son zaman lafiya: Shaikh Zakzaky (H) ba Malamin aƙida ba ne (bai taba kira ga al’umma su rungumi wata aƙida ba). Hadin kan al’umma ne burin shi, saboda haka ne ma cikin mabiyan shi akwai yan kowace mazhaba. Kuma duk shekara ya na hada taron ‘makon hadin kai (unity week)’ inda ake gayyatar malamai da masana daga kowane ɓangare na addini domin ƙarfafa alaƙa da tabbatar da zaman lafiya

Marigayi Sam Nda Isiah, shugaban kamfanin jaridun Leadership (Allah Ya ji qan sa) ya bayyana Shaikh Zakzaky (H) a matsayin “alamin zaman lafiya, mai halin dattaku, wanda Najeriya ke buƙatar irin su” a wata ziyara da ya kai wa Shaikh din a shekarar 2014 bayan kisan ‘ya yan sa 3 da mabiyan sa. Haka zalika, manyan mutane masu daraja sun shaidi Shaikh Zakzaky (H) da wannan halayya ta son zaman lafiya.

A haƙiƙanin gaskiya ma, akwai wani mai son zaman lafiya a Najeriya da ya kai Shaikh Zakzaky (H)? Bawan Allah ɗin da aka kashe masa ‘ya ya har shida rigis, da mabiya fiye da dubu- kuma ake ci gaba da kashe su a kullum, shi kan shi ana tsare da shi da matar sa bisa zalunci, duk da kotu ta ce a sake su; amma duk da haka ko sau daya bai taba kira da a afka ma wani ba, hatta waɗanda su ke zaluntar shi!

A yayin da ya ke cika shekaru 70 da haihuwa, ya ishe shi abun alfahari cewa kimanin shekaru 45 na rayuwar shi ya shafe su wajen kiran al’umma su koma ga tafarkin Allah (T) domin samun tsira ranar alƙiyama. Kari akan haka, shekaru ne da ke cike da albarka duba da irin ayyukan alkhairin da ke cikin su.

Lokacin da ya ke mataimakin shugaba mai kula da al’amuran kasashen waje (international affairs) na ƙungiyar ɗalibai musulmi ta kasa (MSSN), Shaikh Zakzaky (H) ya taimaka wajen assasa wasu ayyukan alkhairi waɗanda har zuwa yau al’umma na amfana da su kamar karatun yara a hutun zango (IVC), wasu karatuttuka na musamman (Daura Ilimiyya), samar da ‘yancin halartar tarukan addini ga mata, ƙarfafa sanya Hijabi ga mata da sauran su.

Waɗanda su ka ƙirƙiri wancan labarin (single story) sun manta su faɗawa mutane cewa Shaikh Zakzaky (H) gatan raunana ne, wanda har yanzu duk watan Ramadan sai ya ciyar da dubunnan mutane mabuƙata. kuma lokaci zuwa lokaci yana aikawa da kayan masarufi zuwa sansanin yan gudun hijira, yana ɗaukar dawainiyar marayu, nakasassu da sauran su.

Madalla da Shehun malamin da labaran ƙarya da ake yadawa akan shi bai hana shi taimakon al’umma ba- har waɗanda ke yaɗa ƙaryar, madalla da shehun malamin da zagi ko tsangwama ba su sanya ya canja daga tafarkin da ya yi imani da shi ba. Madalla da shehun malamin da bai taba gushewa daga yi wa al’umma fatan alkhairi ba. Kamar yanda baya yin wani abu don ya burge ko neman yardar wani.

Ma su iya magana sun ce kowane labari yana da ɓangare guda uku ne: na mai badawa, na wanda ake bayarwa akan shi, da kuma bangaren gaskiya; kuma sai mutum ya saurari ɓangare biyun farko sannan zai iya fahimtar inda gaskiya ta ke. Mutum ba zai taba iya hane haƙiƙanin wanenen Shaikh Zakzaky (H) ba, har sai ya saurari na shi ɓangaren labarin.

An haifi Shaikh Zakzaky (H) a ranar 15 ga watan Sha’aban 1372 a garin Zariya, kuma shi ne na biyar a wajen mahaifin sa Malam Yakub (Allah Ya yi masa rahama), kakannin sa sun zo garin Zariya ne bisa umarnin mujaddadi Shaikh Usman dan Fodio domin su kasance ma su lura da sha’anin karantarwar addini ga al’umma.

Ina taya Shaikh Zakzaky (H) murnar cika shekaru 70 masu albarka. Allah Ya kara masa lafiya da tsawon kwanaki. Allah Ya yi masa sakayya bisa zaluntar shi da ake yi.

Najeeb Maigatari
[email protected]
Jihar Jigawa, Najeriya.