Shan ƙwayoyi da karuwanci suka jawo rufe sansanin ’yan gudun hijira a Maiduguri – Zulum

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Maiduguri 

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana dalilan da suka sa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin rufe sansanonin ‘yan gudun hijira da ke birnin Maiduguri, inda ya ƙara da cewa saboda yadda aka wayi gari baɗalar karuwanci, shan miyagun ƙwayoyi, da makamantan su ne ke neman mamaye matsugunan. 

Har wala yau, gwamnan ya ƙara da cewa, babu wani shugaba mai kishin al’ummar sa da zai zuba ido hakan ta ci gaba da faruwa ga jama’ar da ya ke shugabanta.

Gwamna Babagana Zulum ya bayyana hakan a jawabin murna da sabuwar shekara wanda ya yi wa al’ummar jihar Borno a ranar Asabar da ta gabata, a Maiduguri, babban birnin jihar.

A hannu guda kuma, ya ƙara da cewa bisa al’ada an samar da sansanonin yan gudun hijira ne a lokacin da wutar matsalar tsaron Boko Haram ke tafarfasa kuma domin tsugunar da jama’ar da matsalar ta rutsa da yankunan su, zuwa wani lokaci, amma ba na din-din-din ba.

“Daga cikin matakin rufe sansanonin, za mu ci gaba da kula da yadda abubuwa ke wakana, aiwatar da manufofin da muka ƙudurta tare da gudanar da wasu sauye-sauye idan buƙatar hakan ta taso. Sannan kuma ba mun ɗauki wannan mataki ba ne da wasu manufofi, face kawai domin mu dawo da martaba da ƙimar jama’ar mu.

“Saboda haka ina kira ga al’ummar mu ta jihar Borno, a muhimmin lokaci irin wannan na farawar sabuwar shekara, muhimmin lokaci ne wanda ya dace mu gaya muku bayanai masu ƙarfafa gwiwa tare da karsashi a zukata, wanda nauyin hakan ya rataya a wuyanmu.

“Sannan kuma babban burinmu shi ne samar da ingantaciyar rayuwa tare da bunƙasa tattalin arzikin jihar Borno, ta hanyar kyakkyawar fahimta da goyon baya ga gwamnati. Wanda a 2021 mun yi dukkan abin da ya dace domin ganin tsaro ya inganta ta hanyar bai wa jami’an tsaro da na sa kai goyon baya. Wanda bisa ga hakan kwalliya ta biya kuɗin sabulu.”

Gwamna Zulum ya sake sanar da cewa, ɗaya daga cikin qudurorin gwamnatin sa shi ne ɗaukar matakin rufe ilahirin sansanonin ‘yan gudun hijira da ke faɗin jihar Borno tare da mayar da su garuruwan su na asali.

“Mun rufe sansanonin ‘yan gudun hijrar ne biyo bayan samun ingantaccen tsaro a garuruwan su na asali, tare da dawo da ɗiyauci da martabar jama’armu bakin gwargwado. Saboda mun yi imani kan cewa kowane mutum ya zauna cikin mutunci da ɗiyauci wajibi ne ga kowane ɗan asalin jihar Borno, ko ɗan Nijeriya.

“Sannan mun yi la’akari cewa waɗannan sansanoni na ‘yan gudun hijira sun doshi kasancewa matattarar baɗalar karuwanci, shan miyagun ƙwayoyi da ƙorafe-ƙorafen matsalolin bangar siyasa. Wanda babu wani shugaban da ke kishin jama’arsa zai zuba ido hakan ya na fatuwa ba tare da ɗaukar mataki ba,” inji Gwamna Zulum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *