Shan miyagun ƙwayoyi na neman kassara matasan Nijeriya

A wannan makon, wasiƙata za ta fita ne kai tsaye ga matasa akan batun annobar ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi a tsakanin rukunan al’ummar Nijeriya, domin wata babbar barazana ce da tarnaƙi a ci gaban zamantakewa, tsaro da tattalin arziki. Matsala ce mai wuyar magani wadda a keɓance ɗaya ce daga cikin gagararrun matsalolin da suka gunduri kowa, waɗanda suka tsunduma sabbin jinin shiga mawuyacin hali da yawaitar ayyukan ashsha.

Masana sun tabbatar da cewa al’adar amfani da miyagun ƙwayoyin ba a kan daidai ba, ya na da alaƙar ƙut-da-ƙut wajen yaɗuwar miyagun laifuka a ƙasar nan. Bil hasali, yanayin da ya jawo garƙame matasa da dama gidajen kaso, a cikin lungu da saƙo, a faɗin ƙasar nan. Wanda ko shakka babu, shan miyagun ƙwayoyi tare da dangogin sa ya tsunduma matasan a cikin halin ni’asu.

Sannan duk da matakin da gwamnatoci ke ɗauka wajen yaƙar wannan annoba, ta hanyar kafa hukumomin yaqi da sha tare da fataucin ƙwayoyin, kamar hukumar NDLEA da aka kafa a 1999, da masu alaka da ita, waɗanda ke kai gwauro-mari wajen daqile yaɗuwar lamarin sha tare da safarar ƙwayoyi masu sa maye a ƙasar nan, amma lamarin ya ci tura, ganin har yanzu an kasa kaiwa ga manufar da aka samar dasu.

A halin da ake ciki yanzu, duniya ta na fuskantar babban ƙalubalen mummunan sauyin da waɗannan gagararrun matsaloli, waɗanda ke neman canja alƙiblar matafiyar al’ummar duniyar: shan miyagun ƙwayoyi, safarar mutane, fama da cuta mai karya garkuwar jikin ɗan adam (HIB/AIDS), haɗi da gurɓatar yanayi.

Wanda shan kwayoyi ba bisa ƙa’ida ba da safarar su ke nema ya gagari kundila, sannan kuma barazanar da ke neman karya ƙashin bayan ci gaban matasa a kowacce ƙasa. Matsala ce babba, wadda har yanzu ba a gano lagon ta ba, musamman yadda abin ya fi kamari ga matasa masu jini a jika; ɓangare muhimmi a ci gaba tare da kiyaye diyaucin kowacce ƙasa a duniya.

Kuma kamar yadda masana suka bayyana, shan miyagun ƙwayoyin wata mummunar al’ada ce wadda ta zama ruwan dare a tsakanin kowanne ɓangare na al’umma – maza da mata, yara da manya. Sannan ta’asa ce wadda ta shafi kowanne mataki na al’umma da mu’amalar yau da kullum. Lamarin da ya kaiwa kowa a wuya- saboda bayyanar sa a sarari tare da ɗanɗanar kuɗar sakamakonsa ga al’umma.

A wani bincike wanda cibiyar nazarin amfani da magunguna ba a bisa ƙa’ida ba, kana da gano illolin da hakan ke haifar wa, ta ankarar da cewa tun a tashin farko ana iya gano yadda shan miyagun ƙwayoyi zai yi illa ga rayuwar mutum – a rayuwar matasa, idan sun girma: musamman ga matasan da suka fara ta’ammuli da ƙwayoyi a shekaru 14 – tasirin miyagun ƙwayoyin zai bayyana ne daga shekarun su na 21 zuwa abinda ya yi sama.

Wasiƙa daga RAHMA AHMAD, 09070905293.