Sharhi: Martaba rayuka ita ce yadda ake rungumar manufar “daƙile cutar Covid-19 da zarar an gano ta”

Daga LUBABATU LEI

Har yanzu cutar Covid-19 na ci gaba da yaɗuwa a sassan duniya. A nan ƙasar Sin, cutar nau’in Omicron ta ɓulla a larduna 30 na ƙasar tun daga watan Maris, inda aka ba da rahoton mutane sama da dubu 320 sun harbu da cutar.

A yayin fuskantar saurin yaɗuwar cutar, gwamnatin ƙasar Sin ta jaddada rungumar babbar manufarta ta “daƙile cutar da zarar an gano ta”, wadda ta bayyana yadda ƙasar ke dora al’ummarta da ma rayukansu a gaban kome.

Ƙasar Sin ƙasa ce da ke da al’ummar da yawansu ya kai biliyan 1.4 , daga cikinsu kuma yawan tsofaffi ya kai miliyan 267, kuma ƙasar tana ba da muhimmanci ga batun kare rayukansu da lafiyarsu. A cikin irin wannan yanayi, idan ba a ɗauki manufar “dakile cutar da zarar an gano ta” ba , lallai da wuya a yi zaton irin mummunan hali da ƙasar za ta samu kanta a ciki.

Daga ɗaukar matakin kulle a birnin Wuhan, zuwa ɗaukar kwararan matakai na daƙile cutar a sassan ƙasar da zarar an gano ta, ya sa ƙasar Sin ta yi ta samun nasarar daƙile cutar, kuma hakan ya bayyana manufarta ta kare haƙƙin bil Adam.

Babu shakka, ana fuskantar hasarorin tattalin arziki bisa ga kwararan matakan da aka ɗauka na daƙile cutar, amma kwalliya ta biya kuɗin sabulu, ganin yadda aka kai ga kare rayukan al’umma da ma lafiyarsu.

A sa’i daya kuma, yadda aka kai ga shawo kan cutar yadda ya kamata, ya kuma taimaka ga farfaɗo da tattalin arziki. A shekarar 2020, a yayin da annobar ke addabar tattalin arzikin duniya, ƙasar Sin ce ta fara shawo kanta a duniya, haka kuma ta kasance a kan gaba a duniya wajen farfaɗo da masana’antu da ma tattalin arziki. A shekarar 2021 kuma, tattalin arzikinta ya ƙaru da kaso 8.1% bisa ma’aunin tattalin arzikin GDP.

Kwanan nan, mujallar New Scientist a wani bayanin da ta wallafa, ta bayyana cewa, “Ƙasashen da suka rungumi manufa da ƙa’idojin kawar da covid-19 da zarar an gano ta, su ne mafiya samun nasara wajen yaƙi da cutar, daga rage mutuwar mutane, zuwa bunƙasar tattalin arziki. Idan da a ce ƙasashe da dama sun amince da wannan dabara, da al’ummun duniya sun samu sauƙin cutar.”

Haka lamarin ya ke, manufar “daƙile cutar da zarar an gano ta” ta taimaka ga kare rayuka da lafiyar al’umma mazauna ƙasar Sin. Baya ga haka, manufar ta kuma kiyaye ƙaruwar tattalin arzikin ƙasar, kuma hakan ya kuma samar da gudummawa wajen kiyaye tsarin masana’antun samar da kayayyaki a duniya da ma ƙaruwar tattalin arzikin duniya. Ma iya cewa ƙasar Sin na daga cikin ƙasashen da suka fi samun nasarar yaki da cutar a faɗin duniya, ko ta fannin yawan mutanen da suka harbu da cutar da yawan mutanen da cutar ta halaka, ko kuma ta fannin bunkasuwar tattalin arziki.

Idan kuma muka kalli ƙasashen da suka nuna halin “ko-in-kula” game da cutar, misali a ƙasar Burtaniya, wadda ta sanar da shirin “kasancewa tare da Covid-19” , inda bisa ga shirin aka daina killace waɗanda suka harbu da cutar, kuma gwamnati ma ta daina gano wadanda suka yi cudanya da masu kamuwa da cutar. Amma bisa ga sabuwar ƙididdigar da ƙasar ta fitar, daga cikin ‘yan ƙasar 13, akwai daya da ya/ta harbu da cutar. Sakamakon binciken ya kuma nuna cewa, sakamakon yaɗuwar cutar nau’in Omicron BA.2, mutane ‘yan sama da shekaru 55 da suka harbu da cutar na karuwa cikin sauri tun daga watan Maris, waɗanda suka ninka na baya har sau 20. Masana ma sun yi gargaɗin cewa, tsofaffi sun fi fuskantar haɗarin mutuwa a sakamakon cutar. A ƙasar Amurka kuma, yaɗuwar cutar nau’in Omicron BA.2 ta haifar da ƙaruwar masu harbuwa da cutar, kuma tuni yawan mutanen da cutar ta halaka a ƙasar ya wuce miliyan daya.

Yadda ƙasar Sin take da dimbin al’umma musamman tsofaffi, ya sa ba ta kawar da kai ga cutar ba, in ba haka ba, da wuya a yi zaton hasarorin rayuka da tattalin arziki da za a fuskanta a ƙasar. Kamar dai yadda mujallar New Scientist ta ce, “Ko yadda wasu ƙasashe suka yi watsi da manufar ‘dakile cutar Covid-19 da zarar an gano ta’ na nufin cewa manufar ba ta dace ba? Amsa ita ce lokaci ne kaɗai da ake ganin ceton rayukan al’umma da kiyaye ƙaruwar tattalin arziki bai dace ba.”

Rayuka da lafiya su ne tushen haƙƙin dan Adam, idan babu su, to babu zancen haƙƙin dan Adam ta sauran fannoni. Akwai rashin tabbas ta fannin yanayin cutar da ake fuskanta, amma abu dake zama tabbas shi ne yadda ƙasar Sin ke kare rayukan al’ummarta da ma lafiyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *