Sharhi: Shirme ne yadda aka bayyana ‘yar wasan Xinjiang mai miƙa wutar yula a matsayin martani da Sin ta mayar ga ƙasashen yamma

Daga LUBABATU LEI

Yanzu haka gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na gudana yadda ya kamata a birnin Beijing, wanda ake sa ran za ta zama mai matuƙar nasara a tarihin wasannin Olympics. Kamar yadda akan ce, kyakkyawan mafari shi ne rabin nasara. Bikin buɗe gasar da aka gudanar a daren ranar 4 ga wata har yanzu ya kasance mai burgewa, musamman ma a lokacin da sannu a hankali aka ɗaga wata babbar da’ira mai suffar kasko zuwa sama, a filin gudanar da bikin buɗe gasar, kana ‘yan wasan ƙasar Sin Dinigeer Yilamujiang da Zhao Jiawen suka ɗaga wutar yola tare, inda suka yi tattaki suka miƙa ta tsakiyar da’irar, sa’annan da’irar ta miƙa saman filin wasa mai suffar sheƙar tsuntsu dake birnin Beijing, a matsayin wata alama ta kaddamar da wannan gasa. Hakan ya burge jama’ar kasashe da dama, inda hakan ya nuna tamkar an kunna wutar da ke cikin al’ummar duniya ne, masu hada kai da rungumar makomarsu tare.

Sai dai abin bakin ciki shi ne wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma ba su mai da hankali a kan kyakkyawan sakon da bikin ya isar ga al’ummun duniya, da ma gasar ita kanta ba, a maimakon haka, sun mai da hankali ne a kan ‘yar wasa Dinigeer Yilamujiang, wadda ta fito daga jihar Xinjiang ta kasar Sin, har ma sun riƙa bayyana ta a matsayin martani da ƙasar Sin ta mayar ga ƙasashen yamma waɗanda suka ƙaurace wa gasar.

Kamfanin dillancin labarai na Bloomberg ya ruwaito cewa, “Dinigeer ‘yar wasa ce mai gwaninta, amma bai kamata a ƙyale matsayinta na ‘yar Uygur ba.” Sai kuma mai gabatar da shiri a kafar NBC na Amurka, Savannah Guthrie, wadda a yayin da take bayani ta ce, wannan ya kasance “wata sanarwar da ƙasar Sin ta fitar”, kuma “martani ne da ta mayar ga kasashen yamma”, sai dai furucin ya janyo mata matsala, har ma wasu kafofin yaɗa labarai na ƙasashen yamma suka zarge ta da “bauta wa gwamnatin ƙasar Sin”. Baya ga haka, jaridar NewYork Times ta ce wai an tilastawa wannan ‘yar wasan Xinjiang yin wannan aiki.

Lallai, su waɗannan kafofin yaɗa labarai kwata kwata sun siyasantar da bikin, kamar dai yadda ‘yan siyasar ƙasashen su suka yi tun farkon fari, wato fakewa da sunan kare haƙƙin bil Adam don ƙaurace wa gasar, a wani ƙoƙari na haifar da matsala ga bunƙasuwar ƙasar Sin.

Sai dai a gani na, shirme ne kawai, kuma abun ban dariya ne. Shin ‘yan wasa ‘yan ƙabilar Uygur na Xinjiang ba su cancanci zama masu miƙa wutar yula ta gasar Olympics ba ne? Ko kuma mika wutar yula shi ma wani nau’i ne na aikin keta haƙƙin dan Adam?

Hakan ya sa wasu masu bibbiyar shafukan yanar gizo sun kasa haƙuri, inda suka ce, abun alfahari ne ga ‘yan wasa su kasance masu kunna wuta a bikin buɗe gasar Olympic, don haka shirme ne yadda kafofin yaɗa labarai na ƙasashen yamma suka ce an tilasta wa ‘yan wasan yin hakan. Wasu kuma sun ce, idan babu ‘yan wasan Uygur a wajen bikin, lalle NewYork Times za ta ce, ƙasar Sin ta hana ‘yan wasan Uygur su fito. Lallai kome ya faru ba za ta ji dadi ba.

A game da wannan, kakakin kwamitin kula da wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa (IOC) Mark Adams, ya bayyana a gun taron manema labarai cewa, Dinigeer ‘yar wasan gasar Olympics ta lokacin hunturu ce, don haka tana da haƙƙin halartar dukanin bukukuwan da aka shirya, kuma yadda aka zaɓe ta a matsayin mai miƙa wutar yula, ba shi da alaƙa da inda aka haife ta. A ɗaya ɓangaren kuma, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian ya ce, “An miƙa wutar yula tsakanin zuriyoyi uku, wato tsoffi da masu matsakacin shekaru da kuma matasa, domin nuna gadon ruhin wasannin Olympics, muna farin cikin ganin ‘yan wasan ƙabilu daban daban da suka haɗa da Dinigeer Yilamujiang, sun shiga gasannin da ake gudanarwa, wanda ke nuna cewa, ƙasar Sin tana ƙoƙari matuƙa wajen raya wasan ƙanƙara, da ƙara ƙarfin lafiyar al’ummun ƙasar, wanda kuma ke nuna cewa, ƙasar Sin babban iyali ne dake samun zaman jituwa tsakanin ƙabilu daban daban.”

Daga nata ɓangaren, malama Dinigeer mai shekaru 20 da haihuwa ta ce, “yadda na kasance a bikin buɗe gasar zai dada ba ni ƙwarin gwiwa a kwanaki na gaba, wanda zan riƙe a zuci a tsawon rayuwata.”

Gasar Olympics gasa ce ta wasanni, bai kamata a cusa siyasa a cikin ta ba.

A yayin da annobar Covid-19 ke addabar duniya, yadda ƙasar Sin ta gudanar da gasar kamar yadda aka alƙawarta, ya samar da damar ƙarfafa haɗin kan al’ummun ƙasashe daban daban, don tinkarar ƙalubalen da suke fuskanta, wanda kuma gudummawa ce da ƙasar Sin ta samar wa duniya. Don haka muke lallashin ‘yan siyasa, da kafofin yaɗa labarai na wasu kasashe, da su daina siyasantar da gasar, su mai da hankali a kan sakon da gasar ke isarwa, da ma gasar da ke gudana, kuma in da gaske ne suna “kulawa da” haƙƙin dan Adam na wasu ƙasashe, lallai ya kamata su ƙara nuna sahihancinsu.