Sharhi: Tashar binciken sararin samaniya ta ƙasar Sin, mallakar ƙasar Sin da ma duniya baki ɗaya ce

Kwanan nan, kumbon Shenzhou-14 dake dauke da ’yan sama jannati uku ya dawo doron duniya. Kafin wannan kuma, ’yan sama jannati na kumbon sun yi musayar aiki tare da takwarorinsu dake cikin kumbon Shenzhou-15, wanda aka harba ba da jimawa ba, daga nan kuma, tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin da ake kira “Tiangong”, ta shiga wani sabon mataki na fara gudanar da harkoki daban daban. Kafin wannan kuma, gwamnatin kasar Sin ta taba sanar da bude tashar ga dukkanin kasashe mambobin MDD.

An ce, tun daga shekarar 2016, kasar Sin ta tattara shirye-shiryen gwaji daga wajen kasashe mambobin MDD wadanda suke so su gudanar a tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, kuma kawo yanzu akwai shirye-shirye 9 na kasashe 17, da suka hada da Switzerland, da Poland, da Jamus, da Italiya, da na wasu rukunoni 23 da aka sanya su cikin jerin shirye-shiryen gwajin kimiyya na farko da za a gudanar a tashar.

Darektar ofishin kula da harkokin sararin samaniya na MDD Simonetta Di Pippo, ta bayyana cewa, yadda kasar Sin ta bude kofar tasharta ta binciken sararin samaniya ya kasance wani muhimmin bangare na shawarar MDD ta “binciken sararin samaniya cikin hadin gwiwa”, kuma misali ne abun yabawa.

Sai dai idan an waiwayi baya, Amurka da sauran kasashen yamma sun yi kokarin kafa shingen hana harkokin binciken sararin samaniya da kasar Sin ta gudanar, har ma kasar Amurka ta kafa dokar hana hukumar NASA ta yi hadin gwiwa da kasar Sin, ta hana kasar Sin shiga tashar binciken sararin samaniya ta kasa da kasa. Amma hakan bai hana Sinawa kokarinsu na binciken sararin samaniya ba.

Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da shirin harba kumbuna masu dauke da mutane a ranar 21 ga watan Satumban shekarar 1992, al’ummar Sinawa sun shafe tsawon shekaru 30 suna kokari bisa karfin kansu, har ma hakarsu ta cimma ruwa.

Ci gaban harkokin binciken sararin samaniya na kasar Sin, ba kawai ya shaida karfin kasar a wannan fanni ba, har ma ya sa kaimin ayyukan binciken sararin samaniya na dan Adam baki daya. Yadda kasa da kasa ke hada gwiwa wajen aiwatar da shirye-shirye a tashar bincike ta kasar Sin, zai taimaka wajen tara fasahohi a wannan fanni, da ma ciyar da harkokin binciken sararin samaniya na dan Adam gaba zuwa wani sabon matsayi.

Tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin wadda ta bude kofarta ga kasa da kasa, za ta zama gida na ’yan Adam baki daya a sararin samaniya.

Kamar yadda babban mai tsara ayyukan harba kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin, mista Zhou Jianping ya ce, “Aikin da tashar Tiangong ta sanya gaba shi ne, ya zama dakin gwaji na kasar Sin a sararin samaniya, don tallafawa manazarta kimiyya wajen gudanar da nazari da bincike, don amfanin ’yan Adam baki daya.”

A watan Fabarairun bana, hukumar kula da harkokin sararin samaniya na kasar Amurka (NASA) ta sanar da cewa, tashar binciken sararin samaniya ta kasar za ta daina aiki a shekarar 2030, wadda daga baya za ta fado cikin tekun Pasifik.

Ta haka, muna iya hasashen cewa, nan da shekaru 8 masu zuwa, tashar Tiangong ta kasar Sin za ta kasance tasha irinta daya kacal ta dan Adam, wadda kuma za ta dauki babban nauyin binciken sararin samaniya.

Muna da imanin cewa, tashar za ta hada karfin kasa da kasa, don amfanin dan Adam baki daya, a kokarinta na binciken sararin samaniya.