Sharhi: Yadda Ƙasar Amurka ta nuna fuska biyu a kan batun Taiwan

Daga LUBABATU LEI

A ranar 15 ga watan Nuwamban shekarar 1972, babban taron MƊD ya zartas da ƙuduri mai lamba 2758, kudurin da ya amince da “Gwamnatin jamhuriyar jama’ar Sin ita ce take da wakilcin kasar Sin a MƊD”.

A sa’i ɗaya kuma, ofishin kula da harkokin dokoki na sakatariyar MƊD ma ya bayyana a zahiri cewa, “MƊD na ganin cewa, kasancewarsa wani lardi na ƙasar Sin, Taiwan ba shi da ‘yancin kansa.”

A shekarar 1978 kuma, Sin da Amurka sun cimma yarjejeniyar kulla hulɗar diplomasiyya, inda Amurkar ta amince da gwamnatin jamhuriyar jama’ar Sin a matsayin halastacciyar gwamnati ɗaya kacal a kasar ta Sin, kuma jama’ar Amurka za ta kiyaye hulɗa da jama’ar yankin Taiwan ta fannonin al’adu, da ta kasuwanci da sauransu, amma ban da ta sassan gwamnati.

Baya ga haka, kasashen biyu sun kuma daddale wasu sanarwoyi biyu a shekarar 1972 da ta 1982, inda Amurka ma ta amince da kiyaye manufar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya.

Waɗannan sanarwoyi guda uku dai sun zama tushen hulɗar siyasa a tsakanin ƙasashen biyu.

Sai dai duk da hakan a cikin ‘yan shekarun nan da suka wuce, Amurkar ta riƙa cewa tana martaba manufar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, a yayin da kuma ta yi ta sayar da makamai ga yankin Taiwan, tare da kawar da bayanai na “Taiwan wani ɓangare ne na ƙasar Sin” daga shafin majalisar harkokin wajen ƙasar, baya ga kuma fitar da “dokar hulɗa da Taiwan” da makamantansu, ga shi kuma a kwanan baya, kakakin majalisar wakilan ƙasar ta Amurka Nancy Pelosi, ta kare aniyarta ta ziyartar Taiwan, duk da rashin amincewar da kasar Sin ta nuna da babbar murya.

Lallai, hakan ya shaida yadda babbar ƙasar ta yi amai ta lashe, haka kuma matakin ya zubar da ƙimar ta a idon duniya.

Mai zane: Mustapha Bulama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *