Sharhin fim ɗin ‘Lamba’

Daga HABIBU MA’ARUF ABDU 

Shahararren kamfanin shirya finafinai na Maishadda Global Resources Limited, wanda a baya-bayan nan ya zama kamfani mafi tasiri a masana’antar Kannywood, ya shirya finafinan barkwanci da dama tare da fitaccen Darakta, Ali Gumzak.

Fim ɗinsu na ƙarshe “Ka yi na yi” shi ne wanda ya fi kowanne fim tattara kuɗi yayin haska shi a Sinima a shekarar da ta gabata. 

A wannan sabuwar shekarar ma, sai ga shi sun shigo da wani fim ɗin barkwancin mai suna Lamba.

Fim ne wanda, cikin barkwanci, ya ƙalubalanci yadda jama’a suke yin rayuwar ƙarya musamman a kafofin soshiyal midiya. Ya bada labarin yadda wasu samari uku (Adam A. Zango, Umar M. Sharif da Ado Gwanja) suke bayyana kuɗin ƙarya domin burge ‘yan matan da suke haɗuwa da su a kafofin na sada zumunta. Suna neman irin ‘yan matan nan ne da suke saka hotunansu masu kyau da suka ɗauka cikin salo a kan shafukansu na kafofin sada zumunta.

Ai kuwa sai aka yi rashin sa’a, ashe suma ‘yan matan rayuwar ƙarya da yaudara suke. Duka adon da suke yi da suturu masu tsada, da manyan wayoyin da suke riƙewa, ashe hayarsu suke yi a irin salon nan na ‘OPAY’ a gurin wani ɗan kasuwa mai suna ‘Salo’ (Aminu Shareef Momo). Yadda asirinsu yake tonuwa da kuma abubuwan da suka faru zuwa ƙarshen fim ɗin sun bai wa ‘yan kallo nishaɗi sosai da sosai.

Fim ɗin ya ɗan yi kamanceceniya da wasu finafinai da aka yi a baya (‘Maƙaryaci’ da ‘Kalen Dangi’ wanda dukkansu Ali Gumzak ne ya bada umarnin su a shekarar 2017) amma hakan bai hana shi yin armashi ba. Hasalima fim ɗin barkwanci ne da ba a saba ganin irinsa ba saboda yadda aka saka daɗaɗan waƙoƙi masu tsararriyar rawar zamani har guda uku a cikinsa. Rawar da Adam Zango da Fandy suka yi a waqa ta ƙarshe mai kiɗan cashiya ta burge ƙwarai da gaske.

Haka kuma, saboda buƙatar fim ɗin na samun ’yan wasa da yawa, furodusa (Mai Shadda) bai saka jaruman da ya fi so (M. Shareef da Maryam Yahaya) su kaɗai ba. A wannan karon ya saka Adam Zango tare da wasu jaruman. Hakan ya bada sha’awa saboda dama ’yan kallo sun yi kewar Adam Zangon wanda ba su gan shi a wani babban fim ba tun bayan Ƙarami Sani (Darakta: Falalu Ɗorayi, 2020).

Ado Gwanja, Aminu Sharif (Momo), Maryam Booth, Amal Umar, da Aisha Najamu, suma sun taka muhimmiyar rawa a fim ɗin, yayin da mai fassarar finafinan Indiya, Sultan Abdurrazak, da tauraruwa mai tasowa, Ummi Rahab, da wasu sabbin fuskoki da yawa suka mara musu baya.

Duka jaruman sun nuna ƙwarewa wajen bawa ‘yan kallo dariya, musamman Zango da Ado Gwanja. Umar M. Shareef ma ba a barshi a baya ba. Haka Aisha Najamu (Izzar So) ita ma ta haska sosai, da sauran duka sabbin fuskokin. Ya kamata a yaba wa Darakta (Ali Gumzak), wanda shi ne ya gudanar da su yadda ya kamata.

A taƙaice, koda yake ‘Lamba’ bai samu rubutu mai inganci sosai ba, kyakkyawan fim ɗin barkwanci ne wanda ya yi nasara wajen bada nishaɗi da ban dariya. Tabbas zai ƙayatar da ku, kuma ya bar murmushi mai ɗorewa a fuskokinku. Ku kalle shi!