Sharhin littafin ‘Da Ma Sun Faɗa Mini’

Daga BAMAI DABUWA KKM

Sunan Littafi: Da Ma Sun Faɗa Mini.
Marubuci: Jibrin Adamu Jibrin Rano.
ISBN: Babu.
Shekarar Bugu: 2020.
Yawan Shafi: 200.
Mai Sharhi: Bamai Dabuwa Kkm.

Gabatarwa/Tsokaci.
Babu buƙatar fayyacewa ko bayyana haɗuwa da ƙwarewar wannan littafin ko na marubucin. Don haka ne ma za mu faɗa a taƙaice, wanda na tabbatar ya wadatar: ‘Da Ma Sun Faɗa Min’, shi ne labarin da ya lashe kambu a gasar Gusau Institute ta shekarar 2020.

‘Da Ma Sun Faɗa Min’, labarin wasu ma’aurata ne guda biyu (Zainab da Aliyu). Wanda wani marubuci (Jibril) ya samar a dalilin zaman majalisa daga abokinsa Bashir ɗan Kimiyya. Cukurkuɗaɗɗen labari ne da tarin sarƙaƙiya, ba don salo ko tsaurinsa ba. Sai don yadda yake cike da ƙwarewa da ɗadda bakin duk wani zare da sauƙaƙawa mai karatu hasashe ko kintatar inda aka dosa. Kamar dai yadda ita kanta Zainab ta rikice da hawa kan zargi da mafarke-mafarkenta ta zauna a kan cewa lallai mijinta ɗan ƙungiyar asiri ne kuma ya bayar da fansar abin da za ta haifa wa ƙungiya. Wannan ne ya tilasta mata barinsa. Ta gudu gida wa iyayenta, su kuma suka shigar da Aliyun ƙara a kan lallai sai ya sakar mu su ‘ya. Daga ƙarshe dai gaskiya ta yi halinta. An yi amfani da gamayyar salon bayar da labari a wannan littafin (ciki da waje).

Kura-kurai:

 1. Ƙa’idojin Rubutu:
  Yana daga cikin kuskure mafi girma kuma na farko da ake ankarewa kuma yake da wahalar yafiya ga marubuci idan aka fara da kuskure wa yadda ya kamata a rubuta sunan littafi. Marubucin ya jirkiɗa tare da haifar da ruɗu wa musamman mai karatu yadda ya rubuta sunan littafin a bangon da kuma yadda yake rubuta shi a cikin labarin. A taƙaice, yadda aka rubuta a bangon shi ne daidai fiye da yadda ya zo a shafi na 4 da saura (wanda nan ne labarin ya fara) sakin layi na farko, kamar haka:

“kamar yadda silar samuwar labarin ‘Dama sun faɗa min’.”

Bayan kuskurewa rubuta kalmar daidai, har’ilayau, marubucin ya kuskurewa tsari ko ƙa’idar yadda ake ko ya kamata a rubuta sunan kowanne littafi (wato a fara rubuta kowacce kalma da babban baƙi kamar haka: Da Ma Sun Faɗa Min).

Bayan wannan kuma an kuskurewa wasu kalmomin a rubutun dayawa. Shi kuwa matsalar kiyaye ƙa’idojin rubutu a rubutu na isar da wani saƙon ne na daban ga mai karatu saɓanin nufi ko ainahin sakon da marubuci ke son isarwa. Misali: Ya zo a shafi na 10 kamar haka: “…ta runtuma a guje ta ɓarin damanta da taga ‘yar ƙaramar faraga…” Kalmar taga na nufin ‘window’ ne da Turanci, alhalin abin da marubucin ke son faɗa a wajen shi ne ta ga wato gani ko sukuni. A nan, mai karatu zai sa ya ɗauka ko ta taga ta dira.

Dangane da kala ko adadin kalmomin da aka kuskure wa ƙa’ida kuwa, yawansu ya zarta misali. A ƙalla a kowane shafi na littafin za a ci karo da kimanin kalmomi 4 a shafin farko na labarin, 6 a shafin tsakiya (100) sai kuma kalmomi huɗu a shafin ƙarshe 4 (200). Idan mu ka ɗauki average na duk shafukan littafin (200) da mafi ƙarancin kuskuren kowane shafi daga shafukan (4) wato 200×4 za mu gano cewa an samu kuskuren kimanin kalmomi 800 ke nan a littafin. Ga kaɗan daga kalmomin da aka kufcewa.

• Zata maimakon za ta (4) ×3
• Tashimalam maimako tashi Malam. (5)
• Dena maimakon daina (6).
• Kallonmu maimakon kallon mu (6).
• Bada maimakon ba da (6).
• Naga maimakon na ga (7).
• Rushe-shiyar maimakon rusheshiyar (108).
Da sauransu…

2.0 Kuskurewa Yarda Tsakanin Kalma Da Kalma.
An samu gwaranci da kaucewa lamirin wasu kalmomin alhalin ba su haɗuwa. Misali: “kamar yadda silar samuwar labarin ‘Dama sun faɗa min’ ta zamana…” (4).
A sauƙaƙe kalmar labarin da ta ba za su haɗu ba. Domin guda namiji ne, ɗayan kuma mace.

2.1. Ya zo kana a shafi na 9, kamar haka: “…suna kiran sunanta da wata irin murya mai baan tsoro.”

2.2. Kuskuren Mantuwa Ko Tsallake Wata Kalma Wanda Ya Haifar Da Gwaranci. Ya zo har’ilayau a shafi na 4, sakin layi na farko kamar haka: “wanda kuma taurarin cikinsa ba wasu ba ne face ƙungiyar asirin da suke yi wa amaryar wata takwas…” A sauƙaƙe akwai buƙatar kalmar ‘yan a tsakanin face da ƙungiyar. Kamar dai haka:

‘wanda kuma taurarin cikinsa ba wasu ba ne face ‘yan ƙungiyar asirin da suke yi wa amaryar wata takwas…’

2.3. Ya kuma zo a shafi na 8, kamar haka: “Babu shiri ta kyautar da kanta gami da ƙara sauri tana yi tana sauri.”
Kyautar da kanta ga wa ko me?

 1. Kuskure Wa Bincike Da Saɓa Sunayen Abubuwa Na Haƙiƙa Ko Fassara Daidai.

Marubucin ya yi bakin ƙoƙari wajen bayyana abubuwa na ilmi da shigo da su cikin hikima a labarin. Sai dai, wasu abubuwan da ya shigo da su ya kuskure mu su, domin wasun ba sunansu ke nan ko kuma ya saɓa wa ainashin sunansu. Misali: “Tashimalam ‘Dendoaspis polylepsis'”(5).

Sai kuma ya zo a shafi na 6, kamar haka: “…sunan macijin kasa kenan a kimiyyance.”
Wannan kuskure ne, domin a kimiyyance sunan Kasa shi ne ‘Bitis Gabonica’ (Gaboon Viper). Shi kuwa waccan da marubucin ya kawo wani macijin ne daban ba kasa ba.
https://en.m.wikipedia.org/wiki/Gaboon_viper

3.1. Deja Vu: Marubucin a shafi na 66 – 67 ya fassara da bayyana kalmar Deja vu wanda yadda rubuta kalmar da kuskure (dejavu). Sannan misalin da ya kawo a littafin don fayyace ma’anar kalmar shi ma ya saɓa da ainashin ma’anar kalmar wanda ya kawo shi daidai. Ga yadda ya kawo ma’anar kalmar (wanda yake daidai):
“Dejavu wani irin yanayi ne da mutum yake ji, watarana haka kurum idan wani abu ya faru sai ka riƙa gani kamar ya taɓa faruwa da kai…”

Ya samu kuskure wajen danganta tunanin sani ko jin kalmar IZAGA da Zainab ta yi. A sauƙaƙe, ya sha faruwa da ni inda zan ga an maimaita wani abu da na ke zargin an taɓa yinsa a gabana ko na ji yanayin a jikina. Wani sa’in ma hat nakan kintaci gaban da cewa yanzu kuma wane zai ce abu kaza, kuma sai ya ce ɗin.

Abokina Abubakar Auyo shaida ne a kan wannan yanayin na wa, inda na sha faɗa masa cewa ni fa wasu abubuwan da suke faruwa na ji ko ganinsu a baya. Shi Deja vu kamar maimaici ne na abin da ke wakana kamar dai gaibu ba tuno wani abu da ka sani ko tava ji a baya ba.

3.2. Ya zo kamar haka a shafi na 182, cikin ƙaulin Sulaiman (Likita):
“Ta samu nervous ne haihuwar ta zo mata babu zato…”

Malam ba a samun nervous, zama ake. Ko a Turancin ma cewa suke She’s nervous. Gwaranci ne, kamar dai a Hausa ne idan ka ce ta samu karaya ne da nufin ta karaya.

 1. Kuskure Wa Alamomin Rubutu Da Kamatarsu.
  Duk da cewar an yi amfani da salo biyu ne (ciki da wajen fage) a wannan littafi, kana a tsari salon biyu na bai wa marubucin wasu damammaki na musamman ne. Kamar su kaucewa kufcewar salo da saura. Hakan bai hana marubucin kaucewa wasu abubuwan ba yadda suka kamata. Misali: Ya zo ba ƙaulin taurari (salon ciki), a na mai bayar da labari (waje) kamar haka:

“Me zai faru? Ai tana ɗaga kai ta kalli gabanta…”

Babu buƙatar alamar tambaya a wannan wajen, idan kuwa akwai to akwai buƙatar sa alamar ƙauli ma. A taƙaice misalin kamar misalin:

‘Ganin sun cim mata ne ya sa ta ɗankara ihu!’ Babu buƙatar alamar motsin rai domin ya bambanta da cewa:

“Wayyo!” Ta faɗa da ƙarfi ganin sun cim mata.

 1. Kuskure Wa Azanci Ko Salon Magana.
  Azanci ko salon magana a rubutu na daga ababen da ke armasa labari. A taƙaice ma da su ne ake riƙe mai karatu. Kana yana daga cikin ƙwarewa ko gogewar marubuci idan ya laƙanci yadda ake kamantawa da bambatawa a rubutu kamar yadda shahararren Malami kuma Annabin Adabi ya koyar da mu a Fasaha Cafe, Kaduna 2021. Marubucin ya yi ƙoƙari ainun wajen shigo da su cikin labarin kuma suna hawa. Sai dai a wasu wuraren ya kuskure mu su. Misali: “Kamar yadda ƙudaje ke bin mushen da ke fitar da turirin wari haka suke bin hangamammen bakinsu mai haƙora cako-cako da za su yi saurin tuno maka da bakin manjagara ko tarko.”(9). Kuskuren shi ne ta ya kuma wa suke bi da hangamammen bakinsu?

5.1. Shafi na 10 ƙarshen sakin layi na ɗaya.
“…masu ɗauke da farata cakar-cakar kamar takobi.”

Ko dai caka-caka. Ba wai don kuskure ne cewa cakar-cakar ba, sai don zai bayar da wata ma’anar wanda kuma ya saɓa da takobi. Cakar-cakar na nufin tsini kuma da kaushi-kaushi ko kurji-kurji, bayan mafi akasari takobi tsini da kaifi kawai aka sani.

5.2. Shafi na 18: “ya bi ta da kallo da ɗan dogon cikinta da ya tsufa,…”(an maimaita a shafi na 77). Ko dai ƙato ba dogo ba?

5.3. Abin mamaki, wai matar da a duk lokacin da ta kwanta bacci take mafarkin ana binta za a kashe da cinye ɗan da za ta haifa. Sannan ta gamsar da zuciyarta cewa lallai mijinta ɗan ƙungiyar asiri ne, irin masu cin mutanen nan. Ranar da ta kuma maimaita kalar mafarkin, a ranar ne kuma aka turo wani jirkiɗaɗɗen saƙo wayarsa (ta karanta) kuma ta fahimta da tabbatar da zarginta a kansa cewa, mutane yake ci kuma ya bayar da abin da za ta haifa ne wai za a ce ta kasa guduwa ko fita a gidan saboda tunani ko tsoron dare da duhu. 

“A zuciyarta tana jin tabbas ba don dare ya fara yi ba da ba zata kwana a wannan gidan da shi ba.”(54).

 1. Hausar Baka.
  An samu saɓani da kuskuren rubutu a maimakon daidaitacciyar Hausa a wasu wuraren zuwa Hausar Baka. Wanda hakan ya ci karo da tsari ko ƙa’idar rubutu. Misali:
  • Shashi maimakon sashi (10).
  • Bacin maimakon ban da (18).
  • Harsashensa maimakon hasashensa. (87).
 2. Kufcewar Salo.
  Kufcewar Salo a rubutu na nufi da ɗaukar ma’ana da yawa. A wani wajen yana nufin tufka da warwara ko kuma kama wani zaren labarin da jona shi da wani alhalin ba su da alaƙa. Ko kuma dai, idan aka zaɓi salon bayar da labari a cikin fage, sai a tsinci marubucin da bayarwa a wajen fage ba bisa ƙa’ida ba. A sauƙaƙe, kana da gwari, kufcewar salo na nufin sava ƙa’idar komai a komai. Kamar dai yadda marubucin ya yi: wai a yadda ayyuka da tsare-tsaren kotu suke ne, mutumin da ake ƙara zai saki layi ya tafi bayar tarihin iyaye da kakanninsa. Ba tare da Alƙalin ya katsar shi ba kuma ba. Wannan labarin irin na ‘Yan Sanda ne yayin bincike kafin su aikewa kotu. Ba a zo kotu a shafe shafi sittin ana tatsuniya ba. (Duba shafi na 105 zuwa 164).

 Ga wasu misalan:
7.1. A shafi na 36, ya zo kamar haka:
“Kai ne mutum na farko bayan iyayena da ya nuna damuwarshi cikin dukkan ‘yan’uwa da ƙawayena.” Alhalin a baya, shafi na 34, ya zo kamar haka:

“Nima ina ajin malamai biyu ne suka tashe ta suka tambaye ta abun da yake damun ta saboda ganin yadda hankalinta da nutsuwarta suke yin nisa da ajin…”

7.2. Ya zo kamar haka a shafi na 52 – 53, inda Zainab ta fahimci saƙon da aka turowa Aliyu na huhu baibai duk da kasancewarsa mai siyar da goro. A kallo da fahimtarta kalmar huhu na nufin cikin mutum ne kawai ba na ko goro ba. Kuma domin ɓadda zaren labarin wa fahimtar karatu ko kintace sai marubucin ya bari a haka bai bayyana ba (Hakan kuma ba laifi ba ne, hasalima ana son hakan). Sai dai kuskuren da ya yi a gaba ne shafi na 63, marubucin ya tsaya fayyace ruɗun da Zainab ta shiga alhalin babu buƙatar haka. Domin barin mai karatu a wannan duhun ma suspense ne. Ga wajen:

“Kun san idan mutum ya tsorata da maciji, tsumma sai ya ba shi tsoro. Ba kowa ba ne fa yake kiranta Aliyu neda ya yi mantuwa ya koma gidan ya nemeta… Hatta kafaɗarta da ta ji an dafa shi ya dafa. Amma ita don firgici kawai sai farkawa ta yi ta ga Aliyu da likita a kanta ana ƙara mata ruwa.”(63).

Idan har waccan huhun na nufin na goro ne to fa akwai buƙatar fayyace shi kamar yadda aka fayyace wannan ruɗun da ta shiga wa mai karatu.

Bangon littafin ‘Da Ma Sun Faɗa Mini’

7.3. Ya zo a shafi na 94, kamar haka:
“Kai ne Aliyu?” Aliyu ya gyaɗa masa kai ba tare da ya yi magana ba, shi ma maishari’an sai ya girgiza kai alamar gamsuwa…”

Alqalin ne zai maka magana ka jijjiga masa kai? Ashe ma kai ne Malami.

7.4. “Ba so a ce kun yarda da ni cewa ban kasance irin mutanen da kuke zargi ba…” (104) Me ya sa zai so su yarda bayan bai ƙaryata ba?

 1. Maimaita Kalma Ko Ma’ana (Tautology).
  Ya zo a wurare da dama yadda marubucin ke tsawwala bayani ko maimaita ko ma’ana sama da sauka guda a jimla ɗaya. Gwaranci da kuma gazawa wanda ke haifar da gundura. Misali: “Sai kuma wani salihi a varin zuciyarta ya fara…” 

A nan idan har marubucin na nufin sashe ne da salihi to fa ba su da bambance da kalmar ɓarin. Ke nan ɗaya daga cikin biyun sun wadatar.

8.1. “Haka kuma wannan shi ne…” (105).
Ko marubucin ya fahimta cewa da haka da wannan suna nufin abu guda ne a jimlar. Kawo su duk a jere kuskure ne

8.2. Ya zo a shafi na 97, kamar haka:
“…makeken littafin da ke gaban shi ya fara rubutu kamar wanda aka yi wa gorin cika shi da rubutu.” A nan babu buƙatar sake kawo kalmar rubutu a ƙarshen. Daga cika shin ma an wadatar.

 1. Kuskuren Cusawa Mai Karatu Fahimta Ko Ankararwa Ta Ƙarfi Da Yaji.

A rubutu musamman kalar wanda ake lura ko kiyaye ƙa’idojin rubutu, babu wani dalili ko dokar da ta yarda marubuci ya zaɓi rubuta wata kalma da manyan baƙi ba bisa ƙa’ida ba. Kuma duk muhimmancin kalmar kuwa. Ba daidai ba ne, sannan yana lalata ganɗokin labarin, domin yana sa mai karatu ya tsinkayi inda ake son zuwa. Ya zo a wannan littafin, shafi na 65, kamar haka:

“Ban ga riba ba wajen faɗa miki su waye IZAGA ba kamar yadda ban ga…”

Babu inda doka ta ce a rubuta wata musamman a ƙaulin taurari da manyan baƙi. Yana daga cikin hujjar cewa an yi ne don fargar da mai karatu (wanda ya kasance raina fahimta ko tursasa masa fahimta ta karfi ba don hakan ƙa’ida ko daidai ba ne, yadda a gaba shafi na 183 marubucin ya rubuta kalmar izaga da ƙananan baƙi yadda ya kamata.)

 1. Kuskuren Aiki Da Bugun Littafi.
  Wasu shafukan sun disashe yayin da wasu kuma suka yanke, wanda ya datse wasu kalmomin da wahalar fahimta konkaratu. Misali: 58,71,79,83 da sauran wurare da dama.

Tambayoyi.

 1. Mene ne Dugutsuma (10).
 2. Mene ne Salihi (17).
 3. Ita kam Zainab ba ta sallah ne, ko kuma jini take ko kuma dai an ɗauke wa masu ciki sallah? An bayyana mijinta Aliyu da kula da Sallah sosai (duba shafi na 17). Sannan a shafi na 20, Aliyu a gida ya wuni tare da Zainab. Har ma saboda yadda ta kwanta a kan cinyarsa ta hana masa yin sallar Isha (ke nan ita ma ba ta yi ba 21). A gaba, shafi 52, Aliyu bayan ya kwantar da Zainaba a gado domin ta kwanta yake ce mata zai je ya yi sallar Isha. To ita fa?

Ƙarƙarewa.
Daga ƙarshe, yana da kyau idan mai karatu ya fahimta cewa, zallar ilmi da alfanun da ke tattare da wannan littafin sun zarta adadi da kuma rinjayar kuskuren da muka gano a littafin. Ko ba komai, mun fahimci yadda ake samun ‘yan biyu masu kama ɗaya da kuma bamban. Haɗuwar wannan littafi, ya kai hukuma ta samar da shi a makarantu domin ilmi da sauƙaƙa karatu da bincike. Ina jinjina ga marubucin wannan littafi tare da fatan Allah ya ƙara basira da ilmi mai amfani.

Na gode.

Bamai Dabuwa KKm
07037852514.