Daga NATA’ALA SAMBO BABI (NASABA)
Sunan littafi: Ruɗanin Tunani
Mawallafi: Bello Muhammad Ɗan yaya
Yawan shafuka: shafi 99
Shekarar da aka buga: 2012
Kamfanin da ya buga: Makarantar Hausa
Kamfanin da ya yi ɗab’i: Parresia Press, Ibadan.
Daga farko kamin na shiga a cikin sharhin littafin ‘Ruɗanin Tunani’ zan ɗan cirato wani abu kaɗan daga wasar kwaikwayo na baka da na zube, ko kuma ace wasar kwaikwayo ta Da da ta Zamani, ya alla ko za a fi fahimtar irin namijin ƙoƙarin da aka yi akan samar da littafan wasar kwaikwayo, waɗanda cikin su, har da ‘Ruɗanin Tunani’.
Su dai masana suna ganin akwai dangantaka ƙwarai ta fuskar manufa ko muhimmin saƙon da masanan biyu ke aikawa ga al’umma. (Wato wasar kwaikwayo, na baka da na zube).
Misali anan shine, wasar kwaikwayo na zamani ya qunshi jigogi da yawa acikinsa. Saboda yana tafiya ne da zamani wato marubuta da masana da masu aiwatar da wasar kwaikwayo na zamani, dukkansu suna la’akari ne da abubuwan da zamani ya zo da su, sai su rubuta ko su shirya wasarsu ta kwaikwayo akai.
Wani misali kuma idan ka dubi littafan wasar kwaikwayo sai ka ga yana da saƙo na musamman da yake neman isarwa ga jama’a.
Misali, littafin ‘Kulɓa Na Ɓarna’, yana faɗakarwa ne dangane da irin masu kuɗin nan da ke lalata ‘yan mata. Littafin ‘Zaman Duniya Iyawa’ ne, shi kuwa yana faɗakarwa ne akan Malamai masu hulɗar banza da ɗalibai, haka ma da shuwagabbani da ke hulɗar banza da na ƙasa gare su. Har wa yau, littafin yana faɗakarwa akan ‘yan boko, masu ganin cewar saboda sun yi boko, ba zasu iya bin al’adunsu ba. Yayin da shi kuwa littafin ‘Wasar Marafa’ na gargaɗi ne akan tsafta, shi kuma ‘Zauren Mai Unguwa’ (wanda ake gabatarwa a gidan rediyon Sakkwato) ya na faɗakarwa ne akan sha’anin gwamnati, shi kuwa shirin ‘Yau da Gobe’, an shirya shi ne akan matsalolin daban-dabam, na yau da gobe.
Za a iya cewar duk waɗannan rubuce-rubuce da wasanni, sun taka rawar gani matuƙa ainun, wurin faɗakar da al’umma, kuma a cikin raha. Ni dai a ɗan nazarin da na yi har a yau, banci karo da wanda ya yi rubutu ko wasar kwaikwayo, wanda ya yi bayani akan wannan shaharariyyar matsalar ba, wato saɓanin fahimta, ko kuma ace ‘Ruɗanin Tunani’.
Akan wannan mu na iya cewan littafin rudanin tunani ya yaɗa ko kuma ya yaye duhu ga ‘yan wasar kwaikwayo da marubuta, akan su fahimci haɗa adabin dukka guda uku, Ma’ana, su san cewar wannan shine agabansu, haka ma shine ilimin da jama’a ke buƙatar sani a yanzu.
Haka ma marubuta su fahimci cewa, zai iya yiwuwa a gwama su ayi wasa mai amfani, tunda ga shi littafin ‘Ruɗanin Tunani’ ya nishaɗantar, kuma ya faɗakar da ilmintar da jama’a. Sai dai kuma su sani cewar ba waramin aiki ba ne.
Don haka kuma anan zan shiga a cikin gundarin littafin. Domin na ɗan tsakuro wani abu a cikinsa, don haska wa jama’a kaɗan daga cikin saƙonnin da littafin yake ɗauke da shi.
Tun farko dai a gabatarwar littafin, ta bayana cewa littafin ya fito fili domin yin sulhu dangane da matsalolin da shi kansa ruɗanin tunani ke haifarwa.
Ana iya cewa, tunanin da marubucin ya yi amfani da kalmarsa, irin tunanin nan ne da ka sani, wanda kake yi kai da ƙwaƙwalwarka, ruɗanin kuwa har wayau shine dai wanda ka sani a matsayin ka na bahaushe, ruɗu ko ace (Ruɗewa) ma’ana tunani da ruɗu ne, aka gwamaya kalmomin guda biyu wuri ɗaya don samar da sunan littafin.
Sunan littafin ‘Ruɗanin Tunani’, hakama domin sunan ya auri jigon da aka taka domin cimma manufar da a sanadiyyar ta aka yi rubutun.
Manufar littafin itace, fahimtar da al’umma cewa, akwai wata shaharariyyar matsala a tare da su, matsalar kuwa, da yawa mutane sun fahimceta, da yawansu ba su fahimce ta ba, wato ruɗanin tunani.
Sai dai jama’a gama gari, sun fi kiran wannan matsalar da sunan saɓanin fahimta. Amma a qashin gaskiya, sunan ruɗanin tunani ya fi dacewa da sunanta.
Harwa yau acikin gabatarwar littafin ‘Ruɗanin Tunani’ an taɓo wata magana Wacce ta tilastawa mai karatun littafin dakatawa ya sanya alama domin ci gaba, ma’ana sai ya fahimta da abinda ya karanta a baya, sa’anan daga bisani yaci gaba.
Hakama ya fitar da gaskiyar sakamakon binciken da marubucin ya yi. Marubucin litafi ‘Ruɗanin Tunani’ yana ganin cewar, bahaushen yanzu yana rayuwa akan adabin larabawa da adabin turawa da adabinsa nasa na kansa, (Adabib gargajiya.) Kaga kuwa idan haka ne ashe kuwa marubucin ya yi dai dai da kasaftawar da marubucin ya yiwa al’ummomin har guda uku.
Bahaushe ɗan shekara 90 ya naɗa nasa adabin, xan shekara sittin (60) yana da nasa adabi, hakama ɗan shekara ashirin yana da nasa adabin, kuma kowanne daga cikinsu ya na takama ne da nasa adabin, kuma yana ganin cewar shine dai-dai, haka ma shi yafi dacewa. Kuma dukkanin mutanin nan guda uku suna haɗuwa a sha’ani, to don Allah ya za’ayi a kwashe lafiya.
Dalilin haka, ana iya cewar Samuwar ko samarda wasar kwaikwayo (Film) da rubuce-rubuce akan wannan jigon ya dace ƙwarai da gaske, sai dai ba ƙaramin aiki ba ne, domin dole ga duk wanda zai yi wannan aiki, ya zama masani akan adabin guda uku dukkansu. Waɗanda aka ambata.
Bayan nan kuma, mutum koda masani ne akan adabin uku, to zai ga cewar ba anan gizo ke saƙa ba, ma’ana ya zai yi ya gwama adabin gargajiya da adabin larabawa, adabin turawa, kuma har ya mayar da shi wasar kwaikwayo, kuma har ya nishaɗantar kuma ya fahimtar, ya Ilmintar da faɗakar da al’umma.
Yanzu muna iya cewa kwalliya ta kama hanyar biyan kuɗin sabulu, dalilin bayanar littafin ‘Ruɗanin Tunani’ wanda a cikinsa akwai faɗakarwa, ilmintarwa da nishaɗantarwa. Haka ma kowa zai iya karantawa, kuma ya karu, ma’ana matashi zai iya karantawa, tsoho da yaro, duk za su iya karantawa, namiji da mace, mutumin kauye da mutumin birni, ɗan kasuwa da xan boko, sarki ko talaka.
Amfani da muhimmanci game da mai hankali akan jigon ‘Ruɗanin Tunani’:
Idan ka karanci littafin ‘Ruɗanin Tunani’ za ka gano cewar, haƙiƙa aure yana iya mutuwa saɓanin ‘Ruɗanin Tunani’, mutunci yana iya zubewa sanadiyyar ruɗanin tunani. Haka ma unguwa tana iya ruɗewa sanadiyyar ruɗanin tunani, kai har ma gari yana iya watsewa, duk dai sanadiyyar ruɗanin tunani, ashe tunda haka ne to haƙiƙa wannan matsalar ba ƙarama ba ce.
Wani ƙarin haske kuma shine, shi kansa mai tunani yana iya ruɗewa da tunanin sa. Misali, shi kansa tauraron littafin Rasheed, a farkon littafin shi kansa dubi irin yadda ruɗanin tunaninsa ya yi amfani da shi, dubi irin ruɗewar da ya yi, kuma dole ma ai ya ruɗe, domin babu yadda zai yi ya fahimci kawu audu, kuma ba wani abu da ya kawo saɓanin fahimta a tsakaninsu, illa bambancin adabi da kowa da irin nasa, dubi acan tsakiyar littafin inda Kawu Audu, ya biyo Rasheed kawai sanadiyyar ruɗani (rudanin tunani) sam Rasheed ba zai fahimci Kawu Audu ba, domin daman akwai ruɗani tunani a tsakaninsu.
Ɓangaren kawu audu da amaryarsa ladi, marubucin ya nuna mana cewa, Kawu Audu ya na da zafin kishi, ita kuma Ladi ta gaya wa Kawu Audu cewa, ai duk sati na Allah, Tanko mai albasa tsohon mijinta yana biyowa, kuma yana zuwa can gidan su Ladi, wannan yana nuna cewar har yanzu Malam Tanko bai saki kari ba.
Ka kula da tambayar da Kawu Audu ya yi wa Ladi, mi ke biyowa da Tanko mai Albasa ta wannan hanyar, “ wai ko in dan leko ya ganni” to don Allah yaya za a yi Kawu Audu ya fahimta. Dole Kawu Audu ya ruɗe, acikin ruɗun ne yaro yazo yana tambayar Ladi, kuma a cikin wannan satin ne Kawu Tanko mai Albasa ke biyowa.
Kuma ka dada lura da cewar ruɗanin tunanin ne ya kashe Nafisa har lahira. Hakama Salau bai san sanadiyyar mutuwar Nafisa ba, amma sai ruɗanin tunaninsa ya sanya shi cikin zargi.
Kuma asibiti an ruɗar da likita da ‘yan kallo, hakan ne ya sanya mutanen gari suka ruɗe har jita-jita ta soma, inda har ake ganin wannan taron dai, idan ba gwamna ne ya mutu ba. Kuma wannan taron dai ne ya ruɗar da ɗan sanda, har shima ya gaya wa mai gidansa a waya, kwamishinan ‘yan sanda, shi kuma ya buga wa kwamishinan watsa labarai, ya sanar da shi.
Haka ma meye laifin kwamishinan yaɗa labarai domin ya yi wa gidan ridio da TV da sauran ‘yan jarida, sanarwar mutuwar gwamna, kuma ga shi gwamnan ya ce, zai zo amma bai zo ba.
Ta ɓangaren gwamna da mataimakinsa kuwa dole ne su kashe waya, dalili da ganawar da zasu yi mai matuƙar muhimmanci, dalilin shine, kada jama’a su dame su, su ɗaukar musu hankali, kaga kuwa duk wanda ya kira wayar gwamna ya ji ta a kashe, to haƙiƙa zai ɗauka cewar tabbas gwamna ya mutu.
Haka ma acan baya, marubucin littafin ya ce, mutum yana iya ruɗewa da tunaninsa, akan haka ne ya sa gwamna ya yarda da cewar ya mutu, ko kuma rantsuwa ta kama shi, kuma ma dole ne ya zaci haka, saboda ya yi imanin cewar duk wanda ya yi rantsuwa da wannan Alƙur’anin kuma a bisa karya, tabbas zai mutu. Kamar yadda ya ce da mataimakinsa, “wannan rubutun Gwani Yakubu ne.” “Sa wanda ya rantse da Ƙur’anin akan ƙarya, to ba zai yi awa ɗaya a funiya ba.”
Kammalawa:
Haka ma wani abin burgewa dangane da littafin ‘Ruɗanin Tunani’ shine, fasahar da marubucin ya yi amfani da ita a wajen rufe littafin, anan sai ya sanya tattaunawa tsakanin matar gwamna da likitan maigidanta.
Yadda hirar take shine, likita Sa’idu ya ce, “hajiya na yi tunani na gano cewar, kashi talatin da biyar na matsalolin mutum suna faruwa ne gare shi dalilin ruɗanin tunanin wani akansa.”
Hajiaya ta ce, “munyi daidai! Koda yake ni abin da tunanina ya ba ni shine, kashi talatin da biyar a cikin ɗari na matsalolin da ke faruwa ga mutum, suna faruwa ne a gareshi dalilin ruɗanin wani mutum a kansa.”
Ta ƙara da cewar, “idan dai har tunaninka ya zamo gaskiyan, ni ma ace na wa ya zama gaskiya, za a iya cewa, kashi saba’in a cikin ɗari na matsalolin mutum, suna faruwa ne a gare shi dalilin ruɗanin tunanisa, ko ruɗanin tunanin wani mutum akansa.
Faɗakarwar da take cikin littafin:
Haƙiƙa ni dai faɗakarwar da na lura da ita a cikin karatun littafin ita ce, haƙiƙa duk wanda ya ƙaranci wannan littafin, tabbas idan dai har ya natsar da hankalin sa, to zai yi wa jama’a uzuri, kuma ya riƙa yi wa jama’a musamman Waɗanda suke tare waje ɗaya, ko kuma yanki ɗaya, ya riqa yi musu ɗan ƙarin bayani akan wasu al’ammura waɗanda suka faru gare shi, domin fita zargin su.
Nata’ala Sambo Babi (Nasaba) shine wakilin Mujallar Muryar Arewa a Sakkwato 08063673656, 08096967800