Sharhin wasu baituka na waƙar Ali Makaho mai taken ‘Fahimta’

Daga BAMAI A. DABUWA KKM

Shimfiɗa:

Idan ana maganar rubutu ko waƙa ko kuma aka ce maka Adabi a cure, to ba su da iyaka. Kuma komai daidai ne a harkar. Adabi shi ne madubin rayuwar ɗan Adam. Wato ana kallon rayuwar mutum ne da abin da ke kewaye da shi a rubuta ko a rera shi. Ke nan, kamar yadda yake a zahiri mutane suna sata, caca da sauran laifuka, a Adabi ba zunubi ba ne don ka yi ashariya. A sauƙaƙe, idan akwai wasu mutane da aka yi wa uzurin, ƙarya, batsa da saura to marubuta ne da mawallafa. Kamar yadda manyan masana irinsu Professor Ibrahim Malumfashi suka ayyana, cewa babu wurin addini a Adabi, amma kuma shi zai iya shiga ko’ina.

Har’ilayau, kamar yadda manyan marubuta irinsu Aunty Maimuna Idris Sani Beli suke fayyacewa marubuci shi ne ubangijin littafinsa. Yana iya kashewa ya raya har ma ya yi hisabi ko ya yafe idan ya so. Ke nan, gazawa ce idan aka samu kowane irin rubutu ko waƙa da kuskure a ciki, domin dai bai kamata a samu Ubangiji da kuskure ba. Wannan dalilin ne ya sa ni kuma a ra’ayina nake ganin cewa duk rubutun da aka samu kuskure musamman irin na kufcewar salo to wannan rubutun ya gaza. Wajibi ne ga marubuci ya san komai.

Misali: wani zai iya rasa hikimar Ubangiji na halittar ƙaya, amma ga masu kiwon raqumi sai godiya. Babu wani abu da zaka gani a wannan duniyar da bai da wata fa’ida sai dai ka gaza sani. Marubuci ko mawallafi ba zai iya sanin komai ba har sai ya karanta komai. Amma kuma mutum ba zai taɓa iya sanin komai ba. Sai dai, yana da kyau duk abin da za ka rubuta a littafi ko waƙar ka, kana da cikakken sani a kai. Misali: littafin ‘Yar Tsana na Malam Ibrahim Sheme da a ce za a ba ka karanta, sai ka rantse mace ce ta rubuta, macen ma kuma karuwa. Amma tsantsar bincike ta sa littafin ya haxu.

Ali Makaho, wani shahararren mawaƙin gurmi ne, da ya shahara a zamanin sa. Kamar yadda ya zo bayan sunansa, makaho ne. Kana yana daga hujjar kasancewar sa makaho, idan muka yi la’akari da kirararin da Chali ke masa. “Mai sanda da mutum ɗan Garba.” A makaho aka haife shi, ya mutu yana da shekaru 35 a duniya, sanadiyyar ciwon ciki.

Ka ga dai da gurmi da karatu ba su haɗuwa, amma don sanin cikar kamala ta Adabi, Ali Makaho ba waƙa kawai ya iya ko sani ba ya san Ƙur’ani ma. Kafin mu nausa baitukan, yana da kyau idan muka kalli sunan da ya sa wa waƙar Fahimta. Kalmar Fahimta ba ta buƙatar wata ɗauraya, kowa ma ya san me ake nufi. Amma a sauƙaƙe shi ne, yana nusar da mu cewa waƙar ɗauke take da saƙon da sai an nutsu za a gane. Ga abin da ya ce:

“Laysatul Nasare wa ƙalatil Yahudu.”
Idan ka buɗe Ƙur’ani Suratul Baƙara aya ta 113. Za ka fahimci izgilin ba shi da komai ko madogara da wani yake yi masa ne yake faɗa. Sai kuma a gaba ya ce:
“Kuma ka ce, aule la kafa aule. Summa aule la ka fa aule.”
Duba Suratul Ƙiyama aya ta 34-35.
Wai kuma ya ce da shi Kaico.
Ma’ana: idan ka haɗa baitukan farko da wannan shi ne yake nufin ‘Ka ja can, kai da ba ka da komai.”

Sai shi kuma a gaba ya mayar da martani wa mai yi masa waccan shaguɓen da cewa:
“Ya ayyuhal mudassir.
Ƙum fa anzir.
Wa rabbaka fa kabir.
Wa siyabaka fa ɗahhir.
War-rujza fahjur.
Wa la tamnun tastaksir.
Ta nan haka na gama da arne.”

A nan yana masa nuni da jan hankali ne cewa shi fa ba gafalalle ba ne kamar shi. Yana kiyayewa da tsarkake Ubangijinsa. Don haka ya gama da shi, domin yana tare da Allah.

Lura: kalar wannan karatun ko waƙar mai ɗauke da ayoyi, su ne aka haramta mana yinsu a musulunci.

Allah ka yafe mana duk!

Bamai A. Dabuwa KKM
07037852514
[email protected]