Shari’ar Maina: Kotu ta gayyaci Malami da Magu don su bada shaida

Daga UMAR M. GOMBE

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bada sammaci wanda ya tilasta wa Babban Lauyan Tarayya (AGF), Abubakar Malami SAN, da tsohon shugaban riƙo na hukumar EFCC Ibrahim Magu, da su bayyana a gabanta.

Kotu ta buƙaci ganin waɗanda lamarin ya shafa ne domin su bada shaida a shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, Abdulrasheed Maina.

Kazalika, kotun ta umarci Shugaban Babban Bankin Ƙasa (CBN), Godwin Emefiele da wasu da su bayyana a gabanta a ranakun 9, 10 da 11 na Maris domin bada shaida.

Sauran mutanen da kotun ta kiraye su sun haɗa da: Femi Falana, SAN; M. Mustapha na Bankin Zenith Abuja; Hassan Salihu na hukumar ICPC; G.T. Idriss shi ma daga hukumar ICPC; tsohon kwamishinan ‘yan sanda mai murabus, Mohammed Wakil da kuma Chief Kenneth Amabem.

Sai kuma Manejin Darakta na Bankin UBA, Mr Kennedy Uzoka, Manejin Darakta na Bankin Fidelity, Mrs Nneka Onyeali-Ikpe; Mr Ibrahim Kaigama NIPSS Jos da kuma Daraktan Bin Doka a bankin CBN.