Daga BELLO A. BABAJI
Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya karɓe ƙarar masu zanga-zangar tsardar rayuwa da aka tsare a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, a ranar Juma’a.
Masu zanga-zangar su 75 da ke da shekaru tsakanin 12 da 15 ana tuhumar su ne da laifuka 10 da suka shafi ta’addanci da yunƙurin hamɓarar da gwamnati a lokacin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata a watan Agusta.
Hakan da aka yi ya haifar da yamutsa gashin baki acikin ƙungiyoyin masu zaman kansu da shugabannin adawa waɗanda ke yin alla-wadai da tsare marasa galihu da bincike akan su inda su ke kira ga gwamnati ta waiwayi al’amarin tare samar masa da mafita.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Lateef Fagbemi ya ce akwai ababen da ofishinsa ya kamata ya yi nazari game da su kan batun tare da yanke hukunci.
Ya ce ba huruminsa bane soke umarnin kotu na cigaba da tsare masu zanga-zangar da ɗage sauraron ƙarar zuwa watan Janairu.
Ya umarci rundunar ƴan sanda ta miƙa wa ofishinsa da Daraktan Ofishin Bincike ta Ƙasa (DPPF) takardar ƙarar a ranar Asabar.
Mai Shari’a Oboira Egwuatu wanda ke hukunci game da ƙarar, ya sanya Naira miliyan 10 a matsayin kuɗin belin kowane ɗaya daga cikin masu zanga-zangar tsadar rayuwa 67 cikin 76 da aka tsare.
Waɗanda aka bai wa damar belin ƴan ƙasa da shekaru 15 ne, sannan kowannen su sai ya gabatar da wani ma’aikacin gwamnati a matsayin wanda zai tsaya masa.