Shari’ar masu zanga-zanga: Kwankwaso ya soki ƴan sanda kan tsare ƙananan yara marasa galihu

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alla-wadai da tsare ƙananan yara 67 da ƴan sanda suka yi a Abuja kan zargin su da shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata a watan Agusta.

Kwankwaso ya nuna damuwa matuƙa kan yadda aka bar su babu kulawa sakamakon rashin ba su isasshen abinci, ya na mai kira da a gaggauta ba su kulawa ta lafiya.

Ya ce, hakan ya saɓa wa ƴancinsu na ƴan adam da kuma mutuncinsu, ya na mai cewa kamata yayi a ce su na makaranta ba komar hukuma ba.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya kuma ce wajibi ne gwamnati ta bai wa marasa galihu kariya ba ta cutar da su ba.

A lokacin da ya ke magana game batun belin yaran, Kwankwaso ya ce, bai dace ace yaro ya biya Naira miliyan 10 ba tare nemo jami’in gwamnati da ke mataki na 15 a aiki a matsayin wanda zai tsaya masa.

Ya kuma ce dokar ƴancin yara ta 2003 a sashi na 11, ta nemi da a kare mutuncin kowane yaro ta hanyar kiyaye kulawa da jikinsa, hankalinsa, lamarin raunata walwalarsa, zagin sa, watsi da shi ko wulakanta shi.

Ya yi kira ga hukumomi da su gaggauta sake nazari game da lamarin.