Shari’ar zaɓen shugaban ƙasa: Jam’iyyar Labour ta yi watsi da hukuncin kotu

Jam’iyyar Labour Party ta yi watsi da hukuncin da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa kan ƙarar da ta shigar tana ƙalubalantar nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a babban zaɓen da ya gabata a watan Fabrairu, 2023.

Cikin sanarwar da ta fitar bayan hukuncin da kotun ta yanke a ranar Laraba, Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Obiora Ifoh, ya ce ba a yi wa LP adalci ba kan ƙarar da ta shigar kan jam’iyyar APC da Tinubu.

Ya ce jam’iyyar tasu za ta ɗauki mataki na gaba bayan tuntuɓar lauyoyinta bayan kuma ta amshi takardar shaidar hukuncin da kotun ta yanke.

Ya ƙara da cewa, “Hukuncin bai yi daidai da doka ba kuma ba haka jama’a suka so ba.

“’Yan Nijeriya shaida ne game da maguɗin da aka tafka a zaɓen da ya gudana ran 25 ga Fabrairu, 2023.

“Zaɓe ne wanda duniya baki ɗaya ta yi tir da shi, amma kotun ta ƙi ta amince da abin yake a zahiri.

“Batun dimokuraɗiyya ake yi, kuma ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba har sai jama’a sun yi nasara,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *