Shari’ar Zaɓen Shugaban Ƙasa: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta umarci ma’aikata su zauna gida

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta umarci ma’aikata da su zauna a gida domin kallo da sauraren yadda za ta yanke hukunci kan ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ya zuwa ranar Laraba, 6 ga Satumban 2023.

Babban Akawun kotun, Oluwaleye Oluwasegun David, shi ne ya ba da sanarwar haka a ranar Litinin.

Ɓangarori daban-daban ne suka shigar da ƙara inda suke ƙalubalantar nasarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu a babban zaɓen da ya gabata.

A cewar David, iya waɗanda aka bai wa shaidar shiga za a bari su shiga harabar kotun ranar da kotun za ta yi zaman ya ke hukuncin.

Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da lumana yayin zama na musamman da Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Shugaban Ƙasa za ta yi.

Kotun na shari’a ne kan ƙararrakin da Peter Obi na Jam’iyyar Labour da Atiku Abubakar na PDP da kuma Allied Peoples Movement suka shigar inda suke ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa davya gudana a watan Fabrairun 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *