Shehu Sani, Yero, Hunƙuyi, Sha’aban da wasu jigajigan siyasa sun koma APC a Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamna Uba Sani na Kaduna ya tabbatar wa jigajigan APC 50 da suka dawo jam’iyyar cewa za su mori amfanin zamansu acikinta kamar kowane ɗan jam’iyya.

Sanannu daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar sun haɗa da tsohon gwamnan jihar, Muktar Ramalan Yero; Sanata Shehu Sani; tsohon ɗan takarar gwamnan jihar a jami’yyar NNPP, Sanata Suleiman Hunƙuyi; da tsohon ɗan takarar gwamnan jihar, Alhaji Sani Sha’aban.

Sauran sun haɗa da, Sanata Ɗanjuma Laah, Abubakar Mustapha da kuma Ambasada Sule Buba.

Gwamna Uba Sani ya bayyana jin-daɗinsa ga cigaban da jam’iyyar ta samu, ya na mai cewa babu banbanci tsakanin wanda ya shiga APC a yau da wanda ya shiga shekaru goma da suka gabata.

Ya kuma buƙaci waɗanda suka sauya sheƙar da su faɗa wa magoya bayansu cewa ƙofa a buɗe ta ke ga duk wanda ya ke son shiga jam’iyyar, ya na mai bayyana APC a matsayin jami’yyar da ta samu karɓuwa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Haka kuma gwamnan ya yi alƙawarin cewa za a aiwatar da ayyukan ci-gaba a lunguna da saƙo-saƙo na jihar ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba.

Kazalika, Gwamna Uba Sani ya tunatar da dandazon jama’ar cewa za a yi wa jagorori hisabi game da waɗanda aka ba su ikon mulkar su.