Daga ALI ABUBAKAR SADIƙ
Cikin mutane sama da biliyan takwas da ke raye a wannan duniya tamu a yau, kimanin mutane 722,000 a cikinmu sun sami tsawon rai na kaiwa shekaru 100 cif. To idan zan yi la’akari da wannan ma’aunin kawai, zan iya cewa hakika Sheikh Dahiru Bauchi, na daya daga cikin mutane da Allah ya yi wa wata kebabbiyar baiwa kasancewar ya shiga cikin jerin wadannan mutane da su ka rayu tsawon shekaru dari a duniya.
Na tabbatar kuma idan za’a sake wata kididdigar a cikin wadancan mutane masu shekaru dari a duniya, na tabbatar Shehin dai, zai ciri tuta tsakaninsu saboda Allah ya ba shi ‘ya’ya 100 sukutum. Yawan ‘yayayen ba shine abin mamaki ba, amma kasancewar a cikinsu kaf babu guda daya da ya fandararre.
Makonnin da su ka gabata, wato a ranar 2 ga watan Muharram na Hijira 1446, Sheikh Dahiru Bauchi ya yi bikin cikarsa shekaru 100 a raye, saboda an haife shi a ranar 2 ga watan Muharram na shekarar Hijira 1336 (wato ranar da ta dace da 28 ga watan Yuni na 1927). Allah kadai ya san irin tarin jama’ar da su ka bayar da shaidarsu game da rayuwarsa a garin Bauchi, Najeriya, Afirka da wasu sassa na duniya.
Wannan rubutu ya yi waiwaye adon tafiya a rayuwar wannan dan taliki, wanda aka haifa a karamar hukumar Nafada da ke tsohuwar Jihar Bauchi. Duk da dai yar wannan makala ba ta isa ta kawo dukkan abin fada game da wannan gwarzo ba, domin an buga littafai da shirye-shirye na bidiyo da su kansu ba su wadatar ba.
Kamar yadda Sheikh Khalifa Sani Zaria ya shaida “Zai wahala ka sami wani malami wanda ya yi yawo a lungu da sakon kasar nan da kasashe makwabta domin koyo da koyarwa irinsa” babu karin gishiri cikin zancen Sheikh Khalifa idan mu ka yi la’akari da tsawon shekarun da Malam ya yi na yawon koyo da koyarwa. Ya haddace ƙur’ani a gabann mahaifinsa tun ya na dan karami sannan ya tafi neman karin ilimi a garuruwan Bauchi, Kano da Zaria kafin ya hadu da Sheikh Ibrahim Nyass ya zama almajirinsa a shekarar 1940. Kuma tun daga wancan lokaci zuwa yanzu, kimanin shekaru 80, ya sadaukar da rayuwarsa ga kungiyar Tijjaniyya.
Ya yi auren fari a shekarar 1948 kuma ya sami da guda daya wanda bai yi tsawon rai ba, kuma bayan nan ya dauki shekaru kafin ya sake samun haihuwa yadda har sai da mahaifiyarsa ta fara damuwa, abinda ya saka ta dukufa da yi masa addu’a da saka wasu su taya ta yi masa addu’a. Allah ya karbi addu’arta yadda sai ga shi ya haifi wasu ‘ya’yaye har 100, wato maza 64 da mata 36. Wannan kan sa wata baiwa ce wadda daidaikun mutane Allah ya kebanta da ita.
Babban kalubalen kowane mahaifi shine na tarbiyyar ‘ya’yansa kuma Allah ya sake karawa Sheikh Dahiru Bauchi wata ni’imar inda a cikin ‘yayansa 100, guda 80 sun haddace ƙur’ani. Kafin ya kafa makarantarsa ta karatun ƙur’ani, ya kan tura ‘yayansa zuwa gabas (wato Barno) domin karatun ƙur’ani. Daga baya ya kafa tasa makarantar wadda sannu a hankali sai da ta haifar da kimanin makarantu guda 350 a fadin arewacin Najeriya, da kasar Ghana, Benin da Nijar. Wannan kansa wata ni’ima ce gagara badau da Allah ya sake huwace masa. A kokarinsa na yada karatun ƙur’ani, wani lokaci idan an zo neman yarsa aure ya kan hada da sharadin cewa sai angon ya yarda zai barta ta bude makarantar karatun ƙur’ani a gidanta. Wannan bai hana shi saka ‘yayansa a makarantar boko ba, domin a cikin ‘yayansa akwai masu digirin farko, na biyu har da masu digirin-digirgir.
Sheikh Dahiru Bauchi ya fara karatun tafsiri a shekarar 1952, kuma mutum nawa a duniya su ka sami damar yin tafsiri duk shekara a jere tsawon shekaru sama da 70? Ba ni’ima ba ce? A lokacin da kungiyar Izala ta kunno kai a arewacin Najeriya, daya daga cikin manyan canhe-canje da ta kawo shine yadda aka fara saka tafsirai a gidajen rediyo, wanda a kokarin yan Darika na karbar wannan canji sai su ka fara neman malamin da zai wakilce su wajen yin tafsiri a rediyo. A daidai wannan lokaci kuma sai tsohon shugaban kasar Najeriya, Shehu Shagari, ya mikawa Sheikh Dahiru Bauchi gayyatar ya fara yin wa’azi a fadar gwamnati ta Dodan Barracks. Shehin ya ki karbar wannan gayyata (malamai nawa za su iya haka a yanzu?) ya gwammace ya zama kakakin darikar Tijjaniya a gidan rediyon Najeriya na Kaduna. Sheikh Dahiru Bauchi ya zama murya daya tilo wadda ke kare muradan darikar tijjaniyya, yadda wani ya ba shi sunan Lauyan Tijjaniya, domin a kowanne lokaci a tsaye ya ke wajen kare darikar da akidar ta, ba tare da zage-zage ba, illa dai kafa hujja da ƙur’ani, Sunnna har ma da falsafa.
Alakar Sheikh Dahiru Bauchi da sauran addinai ita kanta abar kwaikwayo ce domin kamar yadda Pastor YD Buru ya shaida cewa a duk shekara ya na gayyatar kiristoci irinsa da irinsu Solomon Dalung a duk azumi zuwa shan ruwa tare da shi, domin jawo sauran masu addinai kusa da rashin nuna kyamata. Kuma ya kan ce musu a koda yaushe, musulmi ke da bashin kiristoci, inda ya kafa hujja da cewa idan ka duba tarihi, yan gudun hijirar musulmi na farko babu inda su ka sami mafaka sai a wajen sarkin Abisiniya, wato Negus, wanda kirista ne, zamanin manzon Allah.
Hatta malamai abokan adawar aƙida irinsu Sheikh Yakubu Yahaya Katsina, ya yabi irin fikirar shehi inda ya ke cewa “Ba abin mamaki ba ne yadda Sheikh Dahiru Bauchi ke iya yin tafsir da ka, ba tare da rike littafi ba, saboda shi gangaran ne a wajen haddar ƙur’ani” abinda ya sha banban da sauran malamai tun tali-tali, wanda wannan fikira na daya daga cikin abinda ya banbanta shi da sauran malamai, ita ma gagarumar ni’ima ce.
Sheikh Dahiru Bauchi malami ne na daban cikin malamai domin bai dogara da harkar makaranta ba kawai, ya na harkokin kasuwanci da noma. Ya yi harkar dab’in littafai, da harkar gidan burodi da harkar safara da siyar da man ja. Ya na da gonaki da dama inda ake noma abinci ba domin sayarwa ba sai don iyalansa da alamajiransa. Akwai gonarsa guda daya da ke garin Gadam a jihar Gombe wadda a ke noma sama da buhu 1000 a duk shekara, ba ya ga daruruwan shanu da ya ke kiwo.
Allah ya huwacewa Shehin damar mallakar daruruwan gidaje a jihohin Bauchi, Kano, Kaduna da Abuja, amma abin da zai baka mamaki shine, babu wani gida da ya ke saka yan haya. Duk gidajensa ya na bada su ga mutanensa su zauna a ciki kyauta. Kamar yadda babban almajirinsa, Malam Yusuf Ibrahim, ya shaida cewa, ‘yayansa da surukansa da wasu almajiransa da su ke zuwa daga kasashe irinsu Ghana, Mali, Burkina Faso, Niger da Sudan ya ke baiwa wadannan gidaje su zauna kyauta.
Ban jin akwai wani malami a raye a yau wanda zai iya tara maka mutane kamar yadda Sheikh Dahiru Bauchi zai tara. Maulidinsa a duk shekara cikakkiyar hujja ce ta hakan domin a duk inda ake irin wannan maulidi, a Bauchi ko a kaduna, za ka samu a ranar garin ya tsaya cak. Duk da irin wadannan tarin baiwa da Allah ya yiwa Sheikh Dahiru Bauchi, ya kasance mutum cikin mutane kalilan da ke da saukin gani fiye da kowa. Kamar yadda Auwalu Zubair, wanda ya hada documentary na bidiyo dinsa ya ce “Na yi interview da sama da manyan mutane 100 a yayin yin wannan aiki amma babu wani cikinsu wanda ya fi Sheikh Dahiru Bauchi saukin gani” ya ci gaba da cewa “Shi Sheikh Dahiru Bauchi ba shi da wata ka’ida ko tsari na kakkange shi daga jama’a (protocol) domin dai duk sallah biyar ya na fitowa masallaci kuma kowa na iya ganinsa bayan an gama sallah kuma babu wanda zai hana ka isa gare shi. Amma saboda tsufa da gajiya, ya kan tafi dakinsa ya kwanta, amma duk da haka, hatta a cikin dakin wasu na shiga har ciki su gana da shi, kungiya-kungiya.
Babban abin sha’awa game da shi shine cewa, duk da tsufansa, bai hana shi halartar jam’in salloli biyar a rana ba, sannan ya saurari mutane bayan sallah. Idan ka ga Shehi ba ya ganawa da al’umma, to ko dai barci ya ke yi, ko kuma karatun ƙur’ani. Saboda hadar-hadar rayuwarsa, ya kan zabi littafan da ya ke son karantawa a duk lokacin da ya ke halin tafiya, ko a mota ko a jirgin sama. A wannan shekara sai da Shehi ya halarci aikin Hajji.
Fa bi ayyi’a la i rabbukuma tukazziban
Yayin da wannan gwarzon Malami Sheikh Dahiru Bauchi ya yi bikin cikar shekaru 100 a ranar 6 ga watan Yuni na shekarar 2024 wanda ya yi daidai da 1 ga watan Muharram na shekarar Hijira 1446 a garin Bauchi, za ku iya yarda da ni idan na ce daidaikun mutane ne a tarihin duniya, su ka sami cikar ni’ima a duniya irin wadda Allah ya albarkaci rayuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi da ita.
Allay ya karo kwanuka masu albarka ya Shehi, ka ci gaba da hidimtawa al’ummarka.
Barkan mu da Jummu’a.
Ali Abubakar Sadeeƙ manazarci ne kuma mazaunin Kano