Sheikh Ɗahiru Bauchi ya gabatar da sallar idi

Daga MU’AZU HARƊAWA

Yayin da galibin al’ummar musulmin Nijeriya ke cika azumi 30 a yau Laraba sannan a tashi da salla gobe Alhami, shi kuwa Sheikh Dahir Bauchi da mabiyansa yau take salla a gare sun inda tuni Sheikh da mabiyansa a Bauchi suka gabatar da sallar Eidul Fitr a. wannan Laraba.

Yayin huɗubarsa, malamin ya ja hankalin mutane da su zauna da juna lafiya, tare da cewa a bar kowa kan ra’ayinsa.

Bayanai daga sakatarorin shehun malamin sun ce Sheikh da mabiyansa sun yi sallarsu a yau ne saboda ganin wata da ya tabatta wanda a cewarsu abin da nassi ya zo da shi kenan maimakon dogaro da fasahar zamani wajen neman wata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *