Sheikh Abduljabbar ya sake sallamar lauyoyinsa a Kotu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Malamin addinin Musuluncin nan da ke Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, ya sake sallamar lauyoynsa a karo na uku. 

A zaman da kotun shari’a da ke Ƙofar Kudu a ƙarƙashin jagorancin, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, wanda ake ƙara bai bayyana da lauyoyinsa ba.  

A zaman na jiya Alhamis, jagoran lauyoyin gwamnati, Nasiru Adamu Aliyu (SAN), ya bayyana da abokan aikinsa 13, yayin da aka ga jagoran lauyoyin wanda ake ƙara, A.O Muhammad (SAN), ya aiko da wasiƙar cire kansa daga cikin shari’ar. 

Gwamnatin Kano na zargin Sheikh Abduljabbar ne da laifin yin kalaman ɓatanci ga addinin Musulunci, zargin da Shehin Malamin ya sha musantawa. 

A lokacin zaman kotun ne Mai Shari’a Sarki Yola ya bayyana cewa: “Kotu ta sami takarda wacce ke ɗauke da kwanan wata 20/4/2022, wacce lauyan wanda ake ƙara A. O Muhammad SAN ya sa wa hannu, inda yake sanar da ni cewa ya fita daga wannan shari’a. A halin yanzu shi ba lauyan wanda ake ƙara ba ne. 

Sai dai wanda ake ƙara, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, ya shaida wa kotu cewa: “Ni ne na nemi su fita daga shari’ar.”

Shaikh Abduljabbar ya ƙara da cewa: “Ba cire kansa ya yi ba, Ni ne na nemi ya cire kan nasa sakamakon takardar ƙorafi da na rubuta zuwa wanda ya haɗa ni da shi, wanda ta ƙunshi bayanin savawar da ya yi da sharuɗan da muka yi yarjejniyar.” 

Ya ƙara da cewa: “Su ma ragowar lauyoyin tare da su, sun gaza kare kansu bisa tuhumar da na yi masu ta haɗin baki na cutar da ni a wannan shari’a. Su ma na nemi su fita daga wannan shari’a. A halin yanzu a shirye nake na cigaba da wannan shari’a.”

Kotun ta nuna wa Shehin Malamin nauyin wannan shariar, tare da haɗarin yin ta ba tare da lauya ba.

Sai ya ce ya samu lauyoyi har uku, sai dai dukkansu sun ce ana yi musu barazana da rayuwa, shi ya sa ba za su iya yin shari’ar ba.

“Na zaɓi a cigaba da yin shariar ne ba tare da lauya ba saboda gudun na yi ta zama a gidan yari, domin sai bayan mun gama magana sai su kira ni su ce rayuwarsu tana cikin hatsari,” inji Malam Abduljabbar. 

Jagoran lauyoyin gwamnati ya bayyana wa kotu cewa sun samu takardar tuhume-tuhumen da Sheikh Abduljabbar ya yi wa lauyoyinsa, sai dai ya yi wa kotun nuni da cewa tun da dukkansu ba sa gabanta, kuma duk wani zargi da za a yi musu zai zama ba daidai ba duba da cewa ba sa nan. Ya kafa hujja da sashe na 36 cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Ya kuma yi bayanin cewa akwai inda ake kai qarar lauyoyi idan ana tuhumarsu, wanda kotun da ake gabatar da wannan shari’a a ciki ba ta da wannan hurumin.

“Idan mutum yana da ƙorafi a kan lauya, akwai hanya da doka ta tanada wanda wannan kotun ba ta da hurumi a kai, bisa haka, sai dai kotu ta shawarce shi ya kai ƙorafin nasa inda ya dace, ” inji Nasiru SAN. 

Ya kuma ja hankalin kotu zuwa sashe na 269 ACJL sakin layi na 4 da ke nuni cewa haƙƙin kotun nan shi ne ta nuna masa hatsarin cigaba da wannan shari’ar ba tare da lauya ba. Ya roƙi kotu da ta ɗauki dayan shawarwarinsa biyu da ya gabatar a kotu kamar haka. 

“Kotu bisa adalci da nuni bisa sashe na 36 na kundin tsarin mulkin ƙasar nan, da ta ba shi dama a wannan karon ya sake ɗaukar lauya, ma’ana kotu ta daga wannan shari’a zuwa wani lokaci don a yi adalci, ko kuma kotu ta yi la’akari da dokar ƙasa ta ‘Legal Aid Act,’ wato dokar agazawa masu yin shari’a a gaban kotu, da ta umarce su su ba shi lauya da zai kare shi bisa dokar,” inji Nasiru SAN. 

Bayan kotu ta saurari dukkan jawaban wanda ake ƙara da masu gabatar da ƙara, ta bayyana cewa batun fitar lauyoyon wanda ake ƙara abu ne da bai shafe ta ba. Kotun ta sake tabbatar da cewa ba hurumin ta bane ɗaukar mataki a kan fitar lauyoyin wanda ake qara. Sai dai ta amince da fitar su sakamakon sun aiko da takarda don sanar da kotun.

Kotu kuma ta yi magana a kan buƙatar da wanda ake kara ya yi na cewa a cigaba da yin shari’ar ba tare da Lauyan ba, alƙalin ya ƙarfafi magana ta biyu da masu gabatar da kara suka kawo cewa kotun ta yi umarni ga (Legal Aid) su ɗaukar wa malamin lauya. 

“Na yi umarni ga Legal Aid su bai wa wanda ake ƙara lauya da zai kare shi, domin hakan akwai fa’ida guda biyu; “Shi lauyan da za a turo wajibinsa ne, kuma ba zai ce shi akwai wata barazana da za ta hana shi tsayawa wanda ake ƙara ba. Fa’ida ta biyu kuma shi ne duk wata wahala ta wannan shari’a, ko kuma wata rashin fahimta da za ta iya faruwa tsakaninsa da wanda ake ƙara, ba shi da damar ya ce ba zai tsaya masa ba.

“Hakan zai hana kawo tsaiko a tafiyar da shari’ar, kuma shi ma wanda ake ƙara ya samu sauƙi, don ba zai biya ko kwabo ba ” inji Alƙali Yola.

A qarshe dai mai Shari’a ya ɗage shari’ar zuwa 26 ga Mayu 2022, don faɗar matsayinsa game da karɓar memori na sautin muryar karatun Sheikh Abduljabbar da aka gabatar da zaman da ya shuɗe.